Connect with us

News

Cutar Kwalera Ta Yi Ajalin Mutum 10 A Adamawa

Published

on

Zazzabin Lassa Cutar ta yi Ajalin Mutum 118 A Cikin Watanni Uku

Gwamnatin jihar Adamawa ta sanar da barkewar cutar Kwalera a jihar inda cutar ta yi ajalin mutum 10 a karamar hukumar Mubi.

A ranar Laraba a garin Yola yayin da yake ganawa da manema labarai kwamishinan lafiyar jihar Felix Tangwami ya ce duk mutanen da suka mutu a dalilin cutar sun mutu ne a gida a maimakon asibiti.

Advertisement

‘Ba Zan Bar Siyasa Ba Har Tsawon Rayuwata’ — Inji Shekarau Yayin Cikar Sa Shekaru 70

Tangwami ya ce gwamnati tare da hadin gwiwar Kungiyar Kiwon Lafiya na Duniya WHO sun dauki matakai domin dakile yaduwar cutar.

“Tun da cutar ya barke muke kokarin mu wajen ganin mun dakile yaduwar cutar.

Advertisement

Kwamishinan ya ce mutanen da suka kamu da cutar da suka je asibiti sun samu sauki inda a ranar 4 ga Nuwanba akwai mutum 25 dake asibiti suna karban magani sannan da dama an sallame su bayan an wayar da kansu kan hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

Ya ce shugaban fannin dakile yaduwar cututtuka da wakilan fannin dakile yaduwar cututtuka na Hukumar NPHCDA na Mubi domin gudanar da bincike kan yaduwar cutar tare da wayar da kan mutane mahimmancin kiyaye tsafta domin guje wa kamuwa da cutar.

Advertisement

A dalilin binciken da suka gudanar jami’an lafiyar sun fara gano wasu daga cikin mutanen da suka kamu da cutar domin tabbatar da cewa sun samu maganin cutar.

Tangwami ya yi kira ga sarakunan gargajiya da su mara wa gwamnati baya wajen wayar da kan mutane mahimmancin gaggauta zuwa asibiti da zaran sun fara rashin lafiya.

Advertisement

Ya kuma kara jadadda mahimmancin tsaftace muhalli, abinci da jiki domin guje wa kamuwa da cutar.

 

Advertisement

 

PREMIUM TIMES

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending