Connect with us

News

Jami’an Yansanda Sun Kama Yan Damfara 6 A Kano

Published

on

Rundunar Ƴansandan jihar Kano ta ce ta cafke wasu mutane shida da ake zargi da hannu a damfara ta hanyar amfani da katin SIM da kuma bayanan bankuna na jama’a.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 5 ga Nuwamba 2025, inda ya ce an gano ƙungiyar ne bayan wani mai suna Nura Abdullahi daga Kabuga ya kai ƙara cewa an sace masa katin SIM kuma aka sace Naira miliyan 5 da dubu 750 daga asusun bankinsa.

Advertisement

Cutar Kwalera Ta Yi Ajalin Mutum 10 A Adamawa

Rundunar ta ce, bincike ya nuna cewa waɗanda aka kama suna yi amfani da bayanan mutane kamar BVN da NIN wajen buɗe asusun banki na bogi, samun kati na ATM, sannan su kwashe kuɗin mutane ta hanyar damfara.

Kazalika Kiyawa ya tabbatar nn gano wayoyin salula guda shida da kuma kuɗi har Naira miliyan ɗaya da dubu ɗari bakwai (N1,700,000) a hannunsu.

Advertisement

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yabawa tawagar masu bincike saboda jajircewarsu da saurin ɗaukar mataki, tare da gargadin jama’a da su guji bayar da bayanansu na BVN da NIN ga wanda ba su sani ba.

Ya ƙara da cewa bincike yana ci gaba, kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending