News
Yara Biyu Sun Mutu A Rijiya A Kano
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar yara biyu da suka faɗi rijiyoyi a lokuta daban-daban cikin kwanaki biyu da suka gabata.
A cewar sanarwar da mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a yau Laraba, 5 ga Nuwamba, 2025, lamarin farko ya faru ne a ƙauyen Kashirmo, ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, inda wata yarinya mai suna Zara’u Muhammad, ƴar shekara 8, ta faɗa cikin rijiya da misalin ƙarfe 8:53 na safiyar Talata.
Hukumar ta ce kafin isowar tawagar ceto daga ofishin babban darakta, mazauna yankin sun yi ƙoƙari su ceci yarinyar amma hakan bai yiwu ba saboda zurfin rijiyar da yawan ruwan da ke cikinta. Bayan isowar jami’an hukumar, an fitar da ita amma daga baya aka tabbatar da mutuwarta, sannan aka miƙa gawarta ga shugaban unguwar, Abdullahi Garba.
Haka kuma, hukumar ta ce ɗaya lamarin na biyu ya faru ne da misalin ƙarfe 10:02 na safiyar yau Laraba a unguwar Dandishe Tsamiyar Goodluck, cikin ƙaramar hukumar Dala, inda wani yaro mai suna Ahmad Abdurashid, mai shekara shida, ya faɗi rijiya.
Jami’an hukumar sun ceto shi amma daga baya aka tabbatar da rasuwarsa. An miƙa gawarsa ga mahaifinsa, Abdurashid, a unguwar Dandishe.
Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, ya yi kira ga iyaye da al’umma su daina tono rijiyoyi a bakin hanya musamman a karkara, tare da rufe rijiyoyin da aka riga aka tona domin kare yara daga fadawa cikinsu
