News
Hukumar FCCPC Ta Rufe Shaguna 20 Kan Zargin Cin Zarafın Masu Saye Da Rashin Cika Ma’auni A Kano
Hukumar kula da gogayyar kasuwanci da Kare Hakkin Masu Saye ta Tarayya FCCPC ta rufe akalla wuraren ajiyar kayyaki da shaguna guda 20 na yadi da shaddodi da Atamfofi a sassan jihar Kano saboda zargin yin kasuwanci na yaudara da tauye ma’auni.
Hukumar ta bayyana cewa an kama ‘yan kasuwar suna sayar da kayan da ba su cika ma’auni na tsawo ko fadi da aka rubuta a jiki ba, wanda ya sabawa tanadin dokar kare hakkin masu saye ta shekarar 2018
Jami’an hukumar sun kai samame ne a yankin masana’antar Sharada da wasu wuraren kasuwanci, inda suka gano wasu ‘yan kasuwa suna sayar da yadudduka da shaddodi da atamfofi da ba su kai tsawon da aka rubuta a jikin su ba.
A cewar Daraktar Sashen Bincike da Lura da Ayyukan Kasuwa na hukumar, Boladale Adeyanka, an gudanar da wannan samame bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa wasu ‘yan kasuwa na yin yaudara wajen sayar da kaya.
“Mun gano yadudduka da aka rubuta a jiki cewa tsawonsu ‘yarfa 10 ne, amma da aka auna sai ya zama 9. Haka kuma akwai wasu da aka rubuta ‘yarfa 5, amma sun kai 4 da rabi kacal,” in ji ta.
Ta ce wannan lamari ya saba wa tanadin Dokar Kare Hakkin Masu Saye ta 2018.
“Sashe na 123 da 125 na dokar FCCPA suna hana kowanne dan kasuwa yin ikirarin ƙarya game da adadi ko farashin kaya, ko yin abin da zai ruɗi masu saye,”.
