News
Jihar Yobe Ta Rufe Dukkan Makarantun Kwana Sakamakon Ƙaruwar Matsalar Tsaro
Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na kwana a fadin jihar, saboda kara tabarbarewar tsaro a wasu sassan Najeriya.
Mamman Mohammed, Daraktan Hulda da Jama’a na Gwamnan Jihar Yobe, ya ce:
“Gwamnatin jihar ta umarci rufe dukkan makarantun sakandare na kwana domin tabbatar da tsaron dalibai.”
Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Tiktoka Da Ta Ƙirƙiri Labarin Sace Ta Don Ƙara Samun Mabiya
Sanarwar ta bayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan taron tsaro da gwamnan, Mai Mala Buni, ya yi tare da shugabannin tsaro, inda aka duba hare-haren da ake kaiwa makarantun a wasu sassan kasar.
Yobe na cikin jihohin da suka rufe makarantu saboda tsaro. A kwanakin baya, jihohi kamar Kebbi, Plateau da Kwara sun dauki matakin rufe makarantu.
A ranar Litinin da ta gabata, ‘yan bindiga sun sace dalibai 24 a Kebbi, yayin da a Neja aka sace dalibai kusan 315 a mako guda. A lokaci guda, wasu ‘yan bindiga sun kai hari coci a Kwara, inda suka sace mutane da dama tare da kashe wasu biyu.
