News
“Na Sacci Indomie Don ‘Yan Matana, Amma Sun Yi Watsi Da Ni A Kurkuku – Matashi Ya Koka”
Usama Abdullahi, matashi mai shekaru 24, wanda aka yanke masa hukuncin shekaru biyu a gidan gyaran hali na Shelleng saboda satar kaya, ya bayyana takaicinsa kan yadda ‘yan matansa uku ba su zo sun ziyarce shi ba tun bayan da aka kama shi.
Usama, wanda ke aiki wajen wanke motoci a ƙaramar hukumar Shelleng, ya ce ya saci fakitin Indomie ne domin rabawa ‘yan matansa. Ya kuma bayyana cewa bayan aikata laifin, ya gudu zuwa wani gari kafin a kama shi.
Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Tiktoka Da Ta Ƙirƙiri Labarin Sace Ta Don Ƙara Samun Mabiya
Ya ce: “Na saci Indomie domin raba wa ‘yan matana uku. Amma tun da aka kai ni gidan gyaran hali, babu ɗaya daga cikinsu da ta ziyarce ni. Saboda haka, ba zan sake kula da su ba idan na fito.”
Lamarin ya jawo hankali kan yadda rashin kulawar iyali ko abokai ke iya shafar matasa masu laifi, musamman lokacin da suke cikin gidan gyaran hali.
DAILY NIGERIAN
