Connect with us

News

Kare Kai Da Al’ummomi Ke Yi Ne Ke Kara Haifar Da Sabbin Rikice-rikice A Filato – Sojin Najeriya

Published

on

An yi wata musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da tawagar dan ta'adda Bello Turji

Rundunar sojin Najeriya ta nuna damuwarta kan yadda wasu al’ummomi a Jihar Filato ke ɗaukar matakan kare kai, tana mai cewa hakan na ƙara jawo sabbin rikice-rikice maimakon magance matsalolin da ake fama da su.

Major Janar MA Etsy-Ndagi, Shugaban Hulda da Al’umma na Sojoji, ya ce barin al’ummomi su kare kansu bai haifar da sakamako mai kyau ba, sai dai ya ƙara ta’azzara rikicin da ake fama da shi a jihar.

Advertisement

Sama Da Mutane Miliyan 24 Sun Kamu Da Cutar Malariya Cikin 2025 A Najeriya  — Gwamnatin Tarraya 

Tun daga shekarar 2001, Jihar Filato na fama da jerin rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya, inda mutane da dama suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata.

Wasu ƙungiyoyi sun yi kira da a ba al’ummomi damar kare kansu saboda hare-haren da ake kai musu.

Advertisement

Sai dai rundunar sojin ta bayyana cewa irin waɗannan matakai na kai-da-kai na haifar da sabbin rikice-rikice da ɗaukar fansa tsakanin al’ummomi. Ta kuma jaddada bukatar kwace makamai, ciki har da waɗanda aka ƙera a gida, daga hannun duk wanda aka samu da su.

 

Advertisement

 

DAILY TRUST

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending