News
Mutane 3 Sun Rasa Rayukansu A Wata Gobarar Tankar Man Fetur A Kano
Akalla mutane uku ne suka rasu sakamakon gobarar da ta tashi bayan kifewar wata motar dakon man fetur a jihar Kano a ranar Juma’a da ta gabata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, kashe gobara ta jihar ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar a ranar Asabar, an bayyana cewa hatsarin ya faru ne misalin ƙarfe 1:30 na rana a mahaɗar kasuwar Kura dake kan titin Zaria.
Kotu Ta Yanke Wa Dalibi Hukuncin Kisa Kan Zargin Kashe Budurwarsa
Rahoton ya ce tankar, mai lambar rijista NGZ 250 XA, ta buge wani direban babur kafin ta kama da wuta. Daga cikin mutane huɗu da abin ya rutsa da su, uku sun mutu, yayin da direban babur ɗin ya tsira da raunuka.
A wani lamari na biyu, wata gobara ta tashi da misalin 2:45 na rana a Hamisu Plaza, kan titin Maiduguri Road, cikin ƙaramar hukumar Tarauni. Gobarar ta cinye shaguna uku a bene kafin jami’an kashe gobara su shawo kan ta, tare da ceto sauran shagunan dake ƙasa.
Daraktan hukumar kashe gobara ta Kano, Alhaji Sani Anas, ya yi kira ga jama’a da su guji sakaci da abubuwan da ke haddasa tashin wuta musamman a wannan lokacin da yanayin sanyi ke shigowa, sannan ya ja hankalin direbobi su bi dokokin hanya don guje wa afkuwar irin waɗannan haɗurra.
