News
An Hallaka Mutane 4, An Jikkata 10 Yayin Gudanar Da Shagalin Bikin ‘Birthday’
Mutane hudu sun rasu, yayin da wasu akalla goma suka ji rauni a wani harin bindiga da aka kai yayin shagalin tunawa da ranar haihuwa a wani banquet hall da ke arewacin birnin Stockton, jihar California.
Ofishin ‘yan sanda na gundumar San Joaquin ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mahari ya bude wuta kai tsaye kan mahalarta shagalin. A cewar jami’an tsaro, har yanzu babu karin bayani kan ko wanene maharin.
Kotu Za Ta Daure Mahaifin Da Ya Kashe ‘Yarsa Saboda Barin Gashin Kanta Babu Lullubi
Duk da yawaitar harin bindiga a jihar, California ta shahara da tsauraran dokoki kan mallakar bindiga. Sai dai, a shekarar 2021, wata kotun tarayya ta soke dokar hana mallakar bindiga irin su AR-15, abin da ya jefa matakan tsaro cikin rudani.
Masu bincike na ci gaba da aiki don gano musabbabin wannan mummunan lamari, yayin da jami’an tsaro ke kira ga jama’a da su rika kiyaye matakan tsaro musamman a wuraren taro.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
