News
An Gurfanar Da Mutum 3 A Kotu Kan Zargin Satar Kaji 500 Da Darajarsu Ta Kai Naira miliyan 9
Rundunar ‘yan sandan Jihar Ekiti ta gurfanar da wasu mutane uku a gaban Kotun Majistare da ke Ado-Ekiti bisa zargin satar kaji 500, wadanda darajarsu ta kai Naira miliyan tara.
Mutanen da ake tuhuma sun hada da Moses Uker (mai shekaru 35), Monday Gambo (32) da Daniel Zakariya (23).
Dakarun Soji Sun Dakile Harin ISWAP Kan Sansanin Soji A Borno, Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Da Dama
Mai gabatar da kara, Insifekta Akinwale Oriyomi, ya shaida wa kotu cewa a ranar 19 ga Nuwamba, a Ado-Ekiti, wadanda ake zargin sun sace kajin mallakin wani mutum mai suna Falade Solomon.
A cewar ‘yan sanda, laifin da ake zargin ya sabawa tanade-tanaden Sashe na 421 da 302(1)(a) na Dokar Laifuffuka ta Jihar Ekiti ta shekarar 2021.
Lauyar kare wadanda ake zargin, Barrista Adunni Olanipekun, ta bukaci kotu da ta ba su beli, tana mai cewa za su mutunta duk sharuddan da kotu za ta gindaya.
Alkalin kotun, Abayomi Adeosun, ya amince da bayar da belin kowanne daga cikin su kan Naira 100,000, tare da masu tsaya musu biyu .
Kotun ta ce dole ne daya daga cikin masu tsayawar ya kasance shugaban kungiyar al’umma a yankinsu.
Kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 30 ga Janairu, 2026.
-
News5 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
