Connect with us

News

Ƙungiyar Dattawan Arewa Ta Ƙalubalanci Shirin Kai Matatar Zinare Lagos

Published

on

images (4)

Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta soki matakin gwamnatin Tarayya na kafa babbar matatar zinare a jihar Lagos, tana mai cewa shirin ya saɓa wa ka’idojin adalci, daidaito da tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata buɗaɗɗiyar wasiƙa da ta aikewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wadda kakakinta, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya sanya wa hannu.

Advertisement

Jami’an ’Yan sanda sun musanta rahotannin sace Kiristoci 170 A Kaduna

A cikin wasiƙar, mai kwanan watan 18 ga Janairu, 2026, NEF ta ce yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya ne ke da mafi yawan arzikin zinare a Najeriya, amma duk da haka ana ƙoƙarin kai babbar cibiyar tacewar ma’adinan zuwa yankin da ba shi da wannan arziki.

Advertisement

“Batun kafa matatar zinare ba lamari ne da ya kamata a yanke hukunci a kai bisa ra’ayin wasu kaɗan ko don jin daɗin wasu ‘yan tsiraru ba. Batu ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya, kuma Arewa na daga cikin yankunan da abin ya fi shafa,” in ji wasiƙar.

Bayanin minista

Advertisement

Ministan Albarkatun Ma’adinai na Najeriya, Dele Alake, ya sanar da shirin kafa matatar zinaren a Lagos ne a yayin wata ganawa da takwaransa na Saudiyya, Ibrahim Al-Khorayef, a ranar 13 ga Janairu.

Sai dai a wata sanarwa da hadimin ministan kan harkokin yaɗa labarai, Segun Tomori, ya fitar, ya ce gwamnatin Tarayya na kuma shirin ƙaddamar da wasu matatun ma’adinai guda uku a wasu sassan ƙasar, ciki har da matatar lithium da ta lashe kusan dala miliyan 600 a jihar Nasarawa.

Advertisement

Hujjojin doka

NEF ta ce shirin kai matatar zinare Lagos ya saɓa wa tanadin sashe na 14(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya haramta fifita wani yanki a kan wani wajen rabon manyan ayyukan ƙasa.

Advertisement

Ƙungiyar ta kuma kafa hujja da sashe na 16(1), wanda ya tanadi cewa dole ne a raba arzikin ƙasa ta yadda kowanne yanki zai amfana, domin tabbatar da walwala, daidaito da adalci.

Matsalolin Arewa

Advertisement

A cewar NEF, jihohin Arewa kamar Zamfara, Kebbi, Neja, Kaduna da Katsina na fama da matsanancin rashin tsaro da lalacewar muhalli, galibi sakamakon haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Ƙungiyar ta ce kafa matatar zinare a ɗaya daga cikin wadannan jihohi zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, rage talauci, da kuma daƙile haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.

Advertisement

Ta buƙaci gwamnatin Tarayya da ta sake nazari kan wannan shiri, tare da la’akari da muradun yankunan da ke da albarkatun zinare, domin tabbatar da cigaba mai ɗorewa da adalci ga dukkan ‘yan Najeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending