Connect with us

News

Wani Ɗaliban Jami’a Ya Rataye Kansa Bayan An Cinye Shi N600,000 A Cacar Kwallon Kafa 

Published

on

Unguwa gawa

Ana zargin wani dalibi ya rataye kansa har lahira saboda an cinye masa Naira 600,000 a wurin cacar kwallon kafa.

Dalibin da ke aji uku a fannin Kimiyar Kwamfuta a Jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida da ke Lapai a Jihar Neja, an gano gawarsa ne a safiyar ranar Litinin.

Advertisement

Gwamnatin Tarayya ta Buɗe Rejistar Neman Guraben Karatu a Ƙasashen Waje na PTDF

Shaidu sun ce ajiyar kudin aka ba wa mamacin, amma ya buga cacar kwallon kafa da su, aka cinye shi.

Advertisement

Majiyoyi sun bayyana cewa wani makwabcinsa ne ya tsinci gawar a rataye a jikin fankar dakinsa, inda aka sanar da hukumomi game da lamarin.

Sace mutane 160 a coci: Taƙaddama ta ɓarke tsakanin hukuma da Ƙungiyar CAN da al’ummar Kajuru

Advertisement

Sojoji sun halaka ’yan ta’adda, sun daƙile harin jirage marasa matuƙi a Borno

Wani dalibi a jami’ar ya shaida wa wakilimu cewa, “Gaskiya ne wani abokin karatunmu ya rataye kansa saboda an cinye kudin hayar da aka ba shi ajiya, a inda ya buga caca da kudin.”

Advertisement

Shugaban Kungiyar Dalibai (SUG) ta Jami’ar, Aliyu Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya bayyana a matsayin abin takaici.

Kakakin ’yan sanda na Jihar Neja, SP Wasiu Abidoun ya shaida wa wakilinmu cewa, da safiyar ranar Litinin suka samu labarin tsintar gawar dalibin mai suna Kelvin Danlami, bayan ya rataye kansa a jikin fankar sama a dakinsa.

Advertisement

“Wani dalibi makwabcinsa da ya gano halin da ake ciki ne ya ankarar da mutane aka garzaya da shi Babban Asibitin Lapai, inda likitoci suka tabbatar ya mutu.

“’Yan sanda na gudanr da bincike domin gano hakikanin abin da ya faru, kuma sun tuntubi iyayen mamacin,” a cewar SP Abiodun.

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending