News
Mutuwar Mai Juna Biyu: ’Yan Sanda Sun Kama Ma’aurata Bisa Gudanar Da Asibitin Bogi A Ondo
’Yan sandan jihar Ondo sun kama wani mutum da matarsa bisa zargin haddasa mutuwar wata mace mai juna biyu a wani asibiti ba bisa ƙa’ida ba da ke garin Ore, ƙaramar hukumar Odigbo.
Marigayiyar ’yar shekara 28, mai suna Iyanu, ta rasu ne bayan an yi mata aikin haihuwa, inda ’yan sanda suka ce sakaci da rashin ƙwarewa ya janyo zubar jini mai tsanani.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abayomi Jimoh, ya ce bincike ya nuna cewa ma’auratan ba su da rajistar aikin likitanci, kuma asibitin da suke gudanarwa haramtacce ne.
’Yan sanda sun ce an tsare ma’auratan, kuma za a gurfanar da su a kotu da zarar an kammala bincike.
Rundunar ’yan sandan jihar Ondo ta kama wani mutum, Kehinde Olawuyi, da matarsa Eniola Olawuyi, bisa zargin haddasa mutuwar wata mata mai juna biyu ’yar shekara 28, bayan da aka yi mata aikin haihuwa a wani asibiti da ke gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba a garin Ore, ƙaramar hukumar Odigbo.
