News
Kano: Ana Sa Ran Haihuwar Jarirai Dubu 600 Zuwa 700 A Shekarar 2026
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ana sa ran haihuwar sabbin jarirai tsakanin 600,000 zuwa 700,000 a shekarar 2026 kaɗai, bisa la’akari da hasashen bunƙasar yawan jama’a da aka yi tun shekarar 2006, wadda ta nuna karuwar al’umma da kaso 3.5 cikin 100 a duk shekara.
Babban sakataren Hukumar Kula da Asibitocin Jihar Kano, Dr Mansur Mudi Nagoda, ne ya bayyana hakan a Kano a ƙarshen mako, yayin bikin yaye ɗalibanKwalejin Kimiyyar Kiwon Lafiya da Fasaha ta Sardauna, a Kano.
Mutuwar Mai Juna Biyu: ’Yan Sanda Sun Kama Ma’aurata Bisa Gudanar Da Asibitin Bogi A Ondo
Dr Nagoda ya yi gargaɗin cewa jihar na fuskantar babban ƙalubale a fannin kiwon lafiya, sakamakon yadda yawan jama’a ke ƙaruwa fiye da adadin ma’aikatan lafiya da ake da su, lamarin da ke ƙara matsin lamba kan asibitoci da cibiyoyin lafiya.
A cewarsa, a halin yanzu jihar na fama da gibin kusan ma’aikatan lafiya 4,000, abin da ke nuni da buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin magance matsalar.
Ya kuma buƙaci cibiyoyin horas da ma’aikatan lafiya da su mayar da hankali kan horaswa ta aikace, domin samar da ƙwararru da za su iya biyan buƙatun al’ummomi, musamman a yankunan karkara.
Dr Nagoda ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na shirin ɗaukar ƙarin ma’aikatan lafiya nan gaba kaɗan, tare da tsara shirin tura su zuwa ƙananan hukumomin da ke fama da ƙarancin hidimomin lafiya, ciki har da Doguwa, Rogo da Sumaila..
