News
Ƴan Sanda Sun Kama Mahaifiya Da Wasu Mata A Wajan siyar Da Tagwayen Jarirai
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Rundunar‘yan sandan jihar Legas ta ce Jami’anta sun yi nasarar kama wasu mata su biyu Ujunwa Una da Chinelo Igbechionwu bisa zargin su da laifin siyar da wasu tagwayen jarirai .
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Benjamin Hundeyin, Shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wani wallafa da ya yi a shafin sa na X @benHundeyin a yau juma’a.
Ya ce rundunar ‘yan sandan ta yi nasarar kamen ne bisa bayanan sirri da ta samu.
“Jami’ain da ke sintiri a sashen Ojodu da ke tashar Berger, daidai kan titin shiga garin Legas su ne suka kama wadanda ake zargin, bayan samun bayanan sirri daga wani mutumi.
“A tare da wadanda aka kama an samu jarirai ƴan biyu mata yan kimanin kwanaki shida a kan hanyar su daga jihar Abia a ranar 9 ga watan Satumba.
“Bincike ya nuna cewa wadanda aka kaman sun kama hanya ne zasu kai jarirai wurin wata ma’aikaciyar jinya a Legas.
“ko da aka tsare su da tambayoyi, nan take suka amsa laifinsu, inda suka bayyana cewa ₦150,000 ne aka biya su kuɗin dauko jariran.
“Wadanda ake zargin sun kara da cewa mahaifiyar jariran ita ta sayar musu da jariran saboda ba za ta iya kula da su ba” in ji Hundeyin.
Yanzu haka dai an mayar da lamarin zuwa sashin kula da jinsi na rundunar, inda daga nan ne aka ajiye jariran a gidan marayu domin kula da lafiyarsu.
Kakakin rundunar ya kara da cewa yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran masu hannu a laifin.
Haka kuma an gurfanar da wadanda ake zargin tun a ranar Alhamis.
