Connect with us

News

Yadda Kanal Ma’aji Ya Kitsa Kutunguilar Kifar Da Gwamnatin Shugaba Tinubu

Published

on

FB IMG 1769712302718

Jami’an binciken sojoji sun gano Mohammed Ma’aji, Kanal a Rundunar Sojin Najeriya, a matsayin babban jagoran yunkurin juyin mulkin da aka yi domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Baya ga kasancewarsa gogarman kitsa, masu bincike sun ce jami’in rundunar infantri ɗin ne ya ɗauki nauyin kuɗaɗen shirya shirin.

Ba a nemi izinin majalisa ba kafin kai harin Amurka a Najeriya – Sanata Ningi

A ƙarshen watan Satumba na 2025 ne hukumomin soji suka fara cafke manyan jami’ai da ake zargi da hannu a yunkurin juyin mulkin, ciki har da Kanal Ma’aji. Zuwa farkon Oktoba na waccan shekarar, an riga an kama jami’ai 16 tare da tsare su dangane da lamarin.

Da farko, shugabannin soji sun ƙi amincewa da cewa akwai yunkurin juyin mulki, suna cewa ana binciken jami’an ne kan “rashin da’a da karya ƙa’idojin aiki.”

Daga bisani, Shugaba Tinubu ya sauke shugabannin rundunonin tsaro, inda ya bar Olufemi Oluyede da Emmanuel Undiendeye kaɗai.

Advertisement

An naɗa Mista Oluyede—tsohon Babban Hafsan Sojin Ƙasa—ya zama Babban Hafsan Tsaro (CDS), ya gaji Christopher Musa, yayin da Mista Undiendeye ya ci gaba da rike mukaminsa na Babban Daraktan Leken Asiri na Tsaro (CDI).

Sai dai a tsakiyar cece-kuce kan zargin kisan Kiristoci da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi, an sake kiran Mista Musa tare da naɗa shi Ministan Tsaro. Ya maye gurbin Muhammed Badaru, wanda ya ce ya yi murabus ne saboda dalilan lafiya.

Bayan watanni biyu, sojoji sun tabbatar da rahoton yunkurin juyin mulkin, inda suka ce jami’an da abin ya shafa za su fuskanci shari’a.

 

Kanal Ma’aji

Majiyoyin soji da suka yi magana da PREMIUM TIMES sun ce masu bincike sun yi imanin Mista Ma’aji ya taka muhimmiyar rawa a matsayin babban mai tsara dabaru, yana haɗa shiri da kayayyakin aiki.

Advertisement

Wata majiya ta ce ya kasance mai tsari sosai, tana ambaton yunƙurinsa a baya na neman a tura shi Ofishin Mashawarcin Tsaro na Ƙasa (ONSA).

“Akwai lokacin da yake neman manyan alaƙa domin a tura shi ONSA,” in ji majiyar, tana ganin hakan na iya zama “ɓangare na shirin.”

Haka kuma, bin diddigin kuɗaɗe ya sanya shi a tsakiyar binciken, a cewar wata majiya.

“Shi ne ke tura kuɗaɗe zuwa ga sauran masu shirin,” in ji majiyar.

Ana duba wata mu’amala ta kuɗi da ake cewa tana da alaƙa da Timi Sylva, tsohon gwamnan Jihar Bayelsa, wanda ake zargin Ma’aji ya daɗe yana hulɗa da shi tun daga shekarunsa na aiki a yankin Neja Delta.

Bayan kama Mista Ma’aji da abokan shirin nasa, masu bincike sun binciki gidan Mista Sylva da ke Abuja, lamarin da ya ƙara zargi kan yiwuwar hannunsa a matsayin ɗan farar hula mai taimakawa shirin.

Advertisement

Sai dai kakakin Mista Sylva, Julius Bokoru, ya musanta zargin a wata sanarwa, yana bayyana ubangidansa a matsayin “dimokiraɗiyya nagari kuma maras ja da baya” wanda ya sha nuna goyon baya ga Shugaba Tinubu.

Majiyoyinmu sun ce waɗanda suka yi mu’amala da Mista Ma’aji tun bayan kama shi sun bayyana shi a matsayin wanda bai nuna nadama ba, kuma yana nuna rashin damuwa ta zuciya yayin da bincike ke gudana. Wata majiya ta ce ba ya bayar da haɗin kai ga masu bincike.

 

Wanene Ma’aji?

Ma’aji, mai lambar aiki N/10668, an haife shi ne a ranar 1 ga Maris, 1976.

Dan asalin kabilar Nupe ne daga Karamar Hukumar Edati a Jihar Niger. Ya fara horon soja a ranar 18 ga Agusta, 1995, kuma ya kammala shi a ranar 16 ga Satumba, 2000, a matsayin ɗalibi na Kwana na 47 a Kwalejin Tsaro ta Najeriya (NDA).

Advertisement

Yawancin ƙwarewarsa ta aiki ya ginu ne a yankin Neja Delta—yanki mai arzikin man fetur—wanda daga baya ya zama muhimmin ginshiƙi ga alaƙar aikinsa da ta siyasa.

Ya halarci Aikin Crocodile Smile II a shekarar 2017, wani babban atisayen Sojin Ƙasa da aka tsara domin magance rikice-rikicen tsageranci, satar mai da matsalolin tsaro a Neja Delta da wasu sassan Kudu maso Yamma.

Ya kuma yi aiki a Depot Nigerian Army, daga baya ya zama Kwamandan Aikin Delta Safe, tare da rike muhimman mukamai na tsaro a lokuta daban-daban.

An ɗaga matsayinsa zuwa Laftanar Kanal a 2013, sannan zuwa Cikakken Kanal a 2017. A lokacin da aka kama shi, jami’in mai shekaru 49 yana rike da mukamin Kwamandan Bataliya ta 19 a Okitipupa, Jihar Ondo.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending