Connect with us

News

NCC Da NSCDC Sun Yi Gargadi Kan Lalata Muhimman Layukan Sadarwa Na Ƙasa

Published

on

f326655d34f84ad747545de93074ff41c5fc1a8157da07b53fe0dc71c1f0a206

Hukumar Kula da Sadarwa ta Nijeriya (NCC) tare da hadin gwiwar Hukumar Tsaron Farar Hula ta Nijeriya (NSCDC) sun gargadi kamfanonin gine‑gine da masu aikin gyaran hanyoyi da su daina lalata layukan sadarwa na fibre‑optic da ke ƙarƙashin ƙasa yayin gudanar da ayyukansu.

Hukumomin sun ce lalata irin waɗannan layuka galibi na faruwa ne sakamakon sakaci ko rashin bin ƙa’ida, inda suka jaddada cewa lalata layukan sadarwa laifi ne kuma masu aikata hakan na iya fuskantar hukunci a gaban kotu.

Advertisement

Doka Ba Ta Bai Wa Jami’an Tsaro Ikon Kama ’Yan Uwan Masu Laifi Ba, Idan Ba A Kama Wanda Ake Zargi Ba — Lauya

A cikin sanarwar haɗin gwiwa, NCC da NSCDC sun bayyana layukan sadarwa na ƙarƙashin ƙasa a matsayin muhimman kadarorin ƙasa, waɗanda ke tallafa wa tattalin arzikin zamani, harkokin kasuwanci da kuma ingantacciyar sadarwar gwamnati.

Advertisement

Hukumomin sun yi gargadin cewa lalata waɗannan kayayyakin more rayuwa na iya jefa tsaron ƙasa, tattalin arziki da lafiyar jama’a cikin hatsari.

Sun ƙara da cewa karkashin Dokar Kare Muhimman Kayayyakin Sadarwa ta Ƙasa (CNII Order 2024), layukan fibre‑optic an ayyana su a matsayin muhimman kayayyakin sadarwa na ƙasar.

Advertisement

Saboda haka, duk wani lalacewa da ya faru sakamakon ayyukan gini ko rashin tuntubar hukumomin da abin ya shafa, na iya zama aikata laifi, kuma duk wanda aka samu da laifi — mutum ɗaya, kamfani ko ɗan kwangilar gwamnati — zai fuskanci hukunci da sauran matakan doka kamar yadda dokokin ƙasa suka tanada.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending