News
Gwamnan Abia Ya Sanya Hannu Kan Dokar Tallafin Tsofaffi
Gwamnan Jihar Abia, Alex Otti, ya sanya hannu kan Dokar Kula da Tsoffi wadda ke ba da gata na musamman ga duk ɗan asalin jihar da ya kai shekara 60 zuwa sama.
Sabuwar dokar ta tanadi:,Albashi na wata-wata kyauta, Jinya kyauta a asibitoci, Sauran alawus-alawus da tallafi har zuwa rasuwa.
An ce manufar dokar ita ce rage raɗaɗin rayuwa ga tsofaffi, da tabbatar da walwalarsu, da kuma basu kariya ta zamantakewa bayan ritaya ko rashin ƙarfi.
Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed, Ya Kori kwamishina
Masu sharhi na ganin matakin zai iya zama abin koyi ga sauran jihohi idan aka aiwatar da shi yadda ya kamata, tare da tabbatar da isasshen kasafin kuɗi da ingantaccen tsari na rarraba tallafin.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
