Connect with us

News

Malam Sulaiman Marafa Ya Karɓi Aiki A Matsayin Manajan Filin Jirgin Sama Na FAAN A  Gombe

Published

on

IMG 20260217 115333 175

Sabon Manajan Filin Jiragen Sama na Hukumar Federal Airports Authority of Nigeria (FAAN) reshen Gombe, Malam Sulaiman Marafa, ya fara aiki a hukumance bayan nadin da aka yi masa kwanan nan.

Malam Marafa ya karɓi ragamar jagoranci ne yayin wani takaitaccen bikin mika ragamar gudanar a filin jiragen sama na Gombe, inda ya yaba da kokarin wanda ya gada bisa yadda ya tafiyar da harkokin tashar tare da kiyaye ingantattun matakan aiki.

Advertisement

Motar Kai Saƙon Kamfanin Amazon Ta Makale A Teku Bayan Direbanta Ya Yi Amfani Da ‘GPS Map’

‎Sabon manajan ya gode wa shugabannin FAAN bisa amincewar da suka yi da shi, yana mai jaddada kudurinsa na inganta yadda ake gudanar da ayyukan tashar da kuma bunkasa ingancin hidimomin sufurin jiragen sama.

Advertisement

‎Ya ce manufofinsa sun yi daidai da tsare-tsaren Gwamnatin Tarayya a bangaren sufurin jiragen sama, yana mai alkawarin yin aiki tukuru domin cimma burin da aka gindaya.

‎Malam Marafa ya kuma bukaci ma’aikatan tashar da su ba da hadin kai tare da aiki cikin kwarewa, ladabi da kuma aiki tare domin samun nasara.

Advertisement

‎Kafin nadin nasa, ya taba aiki a Malam Aminu Kano International Airport, inda ya rike mukamin Manajan Tashar Jiragen Sama ta Kasa da Kasa har zuwa lokacin da aka nada shi Manajan FAAN reshen Gombe.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending