Connect with us

Sports

Yan Real Madrid da suka je Celta buga La Liga

Published

on

Celta Vigo ta karbi bakuncin Real Madrid, domin buga wasan mako na 30 a gasar La Liga ranar Asabar.

Kungiyoyin sun kara ranar 12 ga watan Satumbar 2021 a Santiago Bernabeu, inda Real ta doke Celta Vigo da ci 5-2.

Wadanda suka ci wa Real kwallayen sun hada da Vinicius Junior da Eduardo Camavinga da kuma Karim Benzema da ya zura uku rigis a raga.

Ita kuwa Celta ta ci kwallayenta ta hannun Santiago Mina da kuma Franco Cervi.

Real Madrid tana mataki na daya a kan teburin La Liga da tazarar maki tara tsakaninta da Sevilla ta biyu.

Ita kuwa Celta mai maki 36 tana ta 12 a kasan teburin babbar gasar Sifaniya, bayan karawa 29.

Advertisement

Tuni Real Madrid ta bayyana ‘yan wasan da ta je da su Celta, domin buga karawar.

‘Yan wasan Real Madrid:

Masu tsaron ragaCourtois, Lunin, Diego.

Masu tsaron bayaCarvajal, E. Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Marcelo, F. Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Casemiro, Valverde, Lucas V., D. Ceballos, Camavinga.

Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Bale, Vini Jr., Rodrygo, Mariano.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending