Connect with us

News

DSS Sun Danka Walida Abdullahi Ga Gwamnan  Jigawa Umar Namadi Danmodi

Published

on

1772079206669

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS sun danka matashiya Walida Abdullahi Ibrahim ga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi Danmodi a daren Jiya a hedikwatar Hukumar dake Abuja.

In ba a manta ba dai takaddama ta dabaibaye batun matashiyar mai suna Walida Abdullahi, bayan iyalanta sun zargi wani jami’in DSS mai suna Ifeanyi Onyewuenyi da sace ta daga gidansu tare da tsare ta na tsawon lokaci ba tare da sanin inda take ba.

Advertisement

An Dakatar Da Wani Likita Bayan Da Ya Je Aiki Ya Yi Mankas Da Giya A Kano ‎ ‎

Rahotanni sun ce ana zargin jami’in ya sauya mata addini daga Musulunci zuwa Kiristanci tare da canza mata suna zuwa Chinaza, lamarin da iyalanta suka ce an yi ba tare da yardarta ba ko kuma amincewar danginta kamar yadda jaridar Daily Trust da Aminiya suka wallafa Labarin.

Advertisement

Haka kuma, bayan shafe lokaci mai tsawo a hannunsa, an ce Walida ta haifi jaririya mace, abin da ya kara jawo cece-kuce da damuwa a tsakanin iyalanta da kuma al’umma, musamman dangane da zargin take mata ’yanci da kuma amfani da iko ba bisa ka’ida ba.

Lamarin ya jawo kira daga kungiyoyi da masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam da su ke bukatar gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiya, tare da tabbatar da adalci ga Walida da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi idan har zarge-zargen sun tabbata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending