News
Dakarun Soji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda 20 Ciki Har Da Kwamandan ISWAP A Yobe
Rundunar sojin dake yaƙi da boko haram a Najeriya ta sanar da hallaka kwamandan ƙungiyar ISWAP Abu Yusu tare da wasu dakarun sa akalla 20 a Goniri dake Jihar Yobe.
Mai magana da yawun rundunar Laftanar Kanar Sani Uba ya ce hallaka ƴan ta’addan ya biyo bayan musayar wutar da aka yi da su sakamakon harin da suka kaddamar daren litinin a Goniri.
Muhimman bayanan da jawabin sabon jagoran addini na Iran ya ƙunsa
Kanar Uba ya ce sojojin sun yi nasarra daƙile hare haren a Goniri da Ngamdu, yayin da ya bayyana cewar wasu daga cikin jami’an su ciki harda babban kwamanda sun samu raunuka a artabun.
Kakakin sojin ya ce sun yi nasarar hallaka maharan da kuma kwace makamai da dama, yayin da wasu daga cikin mayaƙan suka gudu.
Kanar Uba ya kuma bayyana kai hari sansanin Timbuktu a kusa da Gwaigomari, inda suka jikkata wasu ƴan ta’addan, kuma yanzu haka sansanin na ƙarƙashin ikon su.
Kakakin sojin ya bayyana aniyar dakarun Haɗin Kai na ci gaba da tabbatar da tsaro da kuma kare lafiyar jama’a a yankin arewa maso gabashin Najeriya, yayin da ya yabawa sojojin dake sadaukar da rayukan su wajen gudanar da aikin.
A jiya Laraba, ministan tsaron Najeriya ya bai wa manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin tafiya yankunan arewa maso gabas da arewa maso yamma domin bunƙasa ayyukan da sojojin ke yi sakamakon ƙaruwar hare haren da aka samu wanda ya kai ga rasa manyan kwamandodi guda 3 a ƙasa da mako biyu.
