Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Kama Tsoho Mai Shekara 74 Da Kilogiram 11 Na Hodar Iblis A filin Jirgin Abuja

Published

on

ndlea 1 1 1 860x491 1 768x438

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta kama wani tsoho mai shekara 74 a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport da ke Abuja, bayan da jami’anta suka gano kilogiram 11 na hodar iblis da aka ɓoye a cikin jakarsa.

Mutumin mai suna Ikwuakalom Nwakoro Emeka ya shiga hannu ne a ranar Asabar a sashen tashin jirage na filin jirgin, yayin da yake ƙoƙarin hawa jirgin British Airways zuwa birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

Advertisement

Magoya Bayan Kwankwasiyya Sun Zargi ‘Yan Daba Masu Alaka Da APC Da Tarwatsa Taron Su A Rogo

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

Advertisement

A cewarsa, jami’an hukumar sun dakatar da mutumin ne yayin binciken yau da kullum da ake yi wa matafiya kafin tashin jirgi. Binciken da aka yi kan kayansa ya kai ga gano hodar iblis da aka ɓoye cikin wasu kayan abinci.

Rahotanni sun nuna cewa an lulluɓe hodar iblis ɗin, wadda nauyinta ya kai kilogiram 11, a cikin fakitin busasshen barkono da aka nika, sannan aka nade su da takardun foil da kuma balan-balan domin ɓoye su.

Advertisement

Babafemi ya ce wannan kama na daga cikin jerin samamen da jami’an NDLEA suka gudanar a sassa daban-daban na ƙasar cikin makon da ya gabata, yayin da hukumar ke ƙara ƙaimi wajen dakile safarar miyagun ƙwayoyi.

 

Advertisement

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending