News
Farashin Kayan Abinci Ya Sauka Da Sama Da Kashi 15 Cikin 100 A Watan Fabrairun 2026
Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta sanar da cewa an samu raguwar farashin kayan abinci da sama da kashi 15 cikin 100 a watan Fabrairun 2026, bayan dogon lokaci na hauhawar farashi a ƙasar.
A cikin rahoton Consumer Price Index (CPI) da hukumar ta fitar a ranar Litinin, an nuna cewa hauhawar farashi a Najeriya ya ragu kaɗan zuwa kashi 15.06 cikin 100 a watan Fabrairu, idan aka kwatanta da kashi 15.1 cikin 100 da aka samu a watan Janairu.
Gwamnatin Kano Ta Musanta Rade-Radin Cewa Sarki Sanusi Zai Jagoranci Hawan Sallah
Rahoton ya ce wannan sauƙi na nuni da raguwar saurin tashin farashin kayayyakin masarufi, kodayake sauyin bai kai matakin da zai kawo babban sauƙi ga al’umma ba.
Sai dai duk da wannan ci gaba, farashin kayayyaki na ci gaba da kasancewa mai tsada ga yawancin ‘yan Najeriya, abin da ke nuna cewa har yanzu matsin rayuwa bai sauƙaƙa sosai ba.
Ana sa ran ƙarin bayani daga rahoton CPI zai ƙara fayyace abubuwan da suka haddasa wannan ɗan sauƙi da kuma hasashen abin da zai iya faruwa a watanni masu zuwa.
-
News7 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
-
News5 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News7 days ago
Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji
