Connect with us

Politics

Zaben 2027: Kungiyar Tinubu Uba Sani Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Dan Buran a Kujerar Sanatan Kaduna Shiyya Ta Daya.

Published

on

Screenshot 20260320 063318~2

A daidai lokacin da zaben shekarar 2027 yake kara karatowa a Nijeriya. Kungiyar magoya bayan Tinubu Da Uba Sani dake yankin Arewacin Nijeriya reshen Jihar Kaduna, sun nuna goyon bayansu ga Dan Buran Zazzau a matsayin Dan takarar Sanatan Kaduna shiyya ta Daya a zaben da ke tafe.

Hakan yana kunshe cikin sanarwar bayan taron shan ruwa da kungiyar ta shiryawa mambobinta a Jihar Kaduna, domin tattaunawa a kan yadda za su tallata tafiyar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2027 mai zuwa.

Advertisement

Kotu Ta Yanke Wa Dillalin Miyagun Ƙwayoyi  Hukuncin Zaman Gidan Gyaran Hali Na tsawon Shekaru 15 A Kano

Da yake jawabi a kan manufofin K kungiyar da inda ta sa gaba, shugaban kungiyar na kasa, Alh. Adamu Muhammad ya ce, “za su mayar da hankali wajen ganin Jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe zaben 2027, ta hanayar fitar da ingantattun ‘yan takara wadanda al’umma ke so kuma gogaggun ‘yan siyasa masu kishi da ci gaban alumma.

Advertisement

Shugaban ya kuma sanar da nuna goyon bayansu ga tsohon dan majalisar tarayya wanda ya wakilci karamar hukumar sabon garin Zaria a shekarar 2003. Kuma tsohon Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin tutar Jam’iyyar ACN a 2011. Sannan tsohon Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a Jam’iyyar APC a 2023. Hon. Mahmoud Sani Sha’aban Dan buran Zazzau a matsayin wanda suke goyon bayan ya nemi kujerar sanata da zai wakilci shiyya ta daya a Jihar Kaduna, wato (Zone One).

IMG 20260320 WA0009

Adamu Muhammad ya ce, “mun cimma wannan matsaya ne bayan la’akari da irin gudunmar da Dan Buran yake bayarwa wajen ci gaban al’umma. Sannan dan siyasa ne da yake da tarin magoya baya tun daga tushe da shauran dalilai da za mu bayyana a nan gaba”.

Advertisement

A Karshe, kungiyar ta jaddada kudirinta na ci gaba da tallata shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da sauran ‘yan takarar Jam’iyyar APC a loko da sako, domin tabbatar da nasararsu a zaben 2027 mai zuwa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending