Connect with us

News

Mawakin Gambara Ya Zama Sabon Firaminista A Nepal

Published

on

afp 69c63d9ed95c 1774599582
Sabon firaministan ƙasar Nepal, Balendra Shah,

Sabon firaministan ƙasar Nepal, Balendra Shah, ya fara aikinsa da salo na musamman bayan an rantsar da shi, inda ya wallafa sakonsa na farko ga al’umma ta hanyar waka mai taken gambara, yana mai kira ga haɗin kai da zaman lafiya a ƙasar.

Shah mai shekaru 35 a duniya, wanda aka fi sani da harkar waka kafin shiga siyasa, ya zama ɗaya daga cikin matasan shugabanni da ke sauya fasalin siyasar Nepal, inda nasararsa ke nuna yadda sabbin ƙarni ke ƙara taka rawa a shugabanci.

Gwamantin Tarraya Za Ta Rufe Layukan Wayoyi A Nijeriya

A cikin sakon nasa, firaministan ya jaddada muhimmancin haɗin kan al’umma domin ciyar da ƙasa gaba, tare da buƙatar jama’a su mara masa baya wajen aiwatar da manufofinsa.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa, zuwan Shah kan wannan muƙami na iya zama wata sabuwar hanya ta kawo sauyi a tsarin shugabanci, musamman ganin yadda yake amfani da fasaha da kere-kere wajen sadarwa da jama’a.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da matasa a ƙasar ke ƙara shiga harkokin siyasa, suna neman kawo canji mai ma’ana a rayuwar al’umma.

Advertisement

 

Aljazeera

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending