News
Auren Bazawara Da Budurwa: Muhawara Kan Zabi Da Fahimta
Batun auren bazawara na ci gaba da haifar da muhawara a tsakanin al’umma, inda wasu samari ke bayyana ra’ayoyi mabambanta kan dacewar ɗaukar mata da suka taɓa yin aure a baya.
Muhammad Ilyas Abdullahi, wanda ya bayyana nasa ra’ayin kan lamarin, ya ce yana ganin zai iya auren bazawara muddin ya gamsu da halayenta, asalinta da kuma rayuwar da ta yi kafin hakan. Ya kuma ƙara da cewa, musamman idan har sun taɓa yin soyayya tun kafin aurenta na farko, hakan na iya ƙara masa fahimta a kanta.
Gobara Ta Tashi A Kamfanin Ganyen Shayin Maya Dake Kano.
Ya ce a wasu lokutan samari na gudun auren zawarawa ne saboda rashin sanin hakikanin dalilan da suka jawo rabuwar aurensu da mazajensu na baya.
A cewarsa, galibi ana dora laifi kan mata ne, ko da kuwa a wasu lokuta mazajen ne ke da alhakin rabuwa.
Muhammad Ilyas Abdullahi ya jaddada cewa kafin yanke shawarar aure, ya dace a yi la’akari da abubuwa kamar shekarun mace, iliminta, halin rayuwarta da kuma ikon ɗaukar nauyin zamantakewar aure.
Sai dai ya kuma bayyana wasu dalilan da ke sa wasu samari ke ƙin auren bazawara, ciki har da ra’ayin cewa auren budurwa na iya samar da sabuwar rayuwa mai sauƙin jituwa. Haka kuma, ya ce wasu na ganin bazawara na iya kwatanta sabon miji da tsohon nata, yayin da ake kallon budurwa a matsayin mai sauƙin karɓar umarni da kuma kunya.
Duk da haka, ya amince cewa akwai zawarawa masu tarbiyya da tausayi, waɗanda matsalolin rayuwa ko cin zarafi daga mazajensu ne suka jefa su cikin rabuwar aure.
A ƙarshe, ya bukaci al’umma da su rika duba halaye da mutunci fiye da tarihin aure, tare da guje wa yanke hukunci cikin gaggawa.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
