Connect with us

Politics

WAI ME GARO YA YI NE? 

Published

on

images (2)

Daga Abba Anwar 

Da fari dai, irin wannan hayaniya da soke-soke da ake yi ya saɓa da asalin manufar da aka kafa jam’iyyar APC. Wacce tun daga farko ta kasance haɗin kan mabambantan ra’ayoyin siyasa domin cimma manufa guda—wato kawar da jam’iyyar PDP daga mulki.

Advertisement

Wannan manufa ta haɗin kai ya kamata a ci gaba da riƙe ta, musamman ganin cewa APC ta shafe sama da shekaru goma tana mulki. Kaucewa wannan ginshiƙi na farko shi ne ya jefa jam’iyyar cikin halin da take ciki yanzu a Kano.

An bayyana zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati tsakanin 2020 zuwa 2023 da suka kai Naira Bilyan 57.4, wanda ya kai ga gurfanar da tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi kuma ɗan takarar Mataimakin Gwamna a zaben 2023, Murtala Sule Garo, a gaban babbar kotun Kano.

Advertisement

Kano: Gwamna Abba Na Shirin Naɗa Murtala Garo A Matsayin Mataimaki — Rahotanni

Babban Alkalin Babbar Kotun jihar Kano dake Miller road, wato Sanusi Ado Magaji bayan ya bibiyi karar da gwamnatin jihar Kano ta shigar kan Garo, sai ya yanke hukuncin cewa ai ita Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, ba ta da hurumin bincike a kan korafin.

Advertisement

Babban Alkalin a takardar yanke wannan hukuncin wacce a ka sanyawa hannu a ranar 30 ga watan Juli, 2025, ya hakaito hukunce-hukunce da a ka taba yi masu kamanni da irin wannan korafin a kan Garo. Bisa dogaro da su irin wadancan hukunce – hukuncen ta sa ya sallami wancan korafin daga kan Garo.

Da ita Kotun ta bayyana cewa hukumar da ta shigar da ƙarar ba ta da hurumin binciken irin waɗannan zargin laifuka, don haka ta yi watsi da ƙarar tare da sallamar waɗanda ake tuhuma. Duk da cewa an ɗaukaka ƙara, wasu na ganin kamar ita gwamnatin jihar Kano din kamar ma ba ta da sha’awa a kan korafin sosai.

Advertisement

Ina da wani kalubale da nake so na jefo a nan. Dan Allah a nuna min wani shahararren dan siyasa a kaf kasar nan, wanda shahararsa ta kai shahara, amma ba shi da wani korafi da a ka shigar a kansa, ko a kotu ko a wata hukumar tuhumar laifuka. Waye shi? Dan Allah a nuna mutum daya kacal. A iya sani na fa na ce. Ban ce babu ba. Amma a karar da ni sani kan hakan.

A bangaren siyasa kuwa, abin mamaki ne yadda wasu manyan ‘yan APC a Kano ke ci gaba da rikici da juna. Kafin zuwan Gwamna Abba Kabir Yusuf cikin APC, jam’iyyar na fama da rikice-rikice masu tsanani na cikin gida. Kai ka ce ba manya a jam’iyyar. Idan har wannan halin ya ci gaba, zai iya sa wa kowa ya fadi ba nauyi.

Advertisement

Da nine gwamnan Kano zan yi iya kokarina wajen ganin na sasanta jiga-jigan jam’iyyar APC dan samun nasarar jam’iyyar. Muddin zai samu ya yi haka, to lallai kuwa tarihin siyasar Kano ba zai taba mantawa da shi ba.

Ina da labarin cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin Garo shi ne mafi dacewa ya zama Mataimakin Gwamna. Musamman saboda wasu dabaru na cin zabe da tsira da mutunci a siyasance. A dalilin haka kuma ya roƙi Gwamnan a yi masa alfarma kan hakan. Ai kuwa nan ma da nine Gwamnan Kano, ai da kuwa ba jira, nan da nan za a ga aiki da cikawa.

Advertisement

Shi fa Garo din nan, shine ya yi wa dan takarar Gwamnan Kano a zaben 2023, wato Maigirma Nasiru Yusuf Gawuna, Mataimaki. Bayan an fadi zaben, maimakon da, a na tunanin Gwamnatin Tarayya, kamar yadda a ka saba a kowace jam’iyya, za a samawa dan takarar Gwamna da Mataimakin sa manyan kujeru a sama, muddin jam’iyya mai mulki ita ce ta wadannan yan takara. Kamar dai yadda ya faru a Kano din da Gwamnatin APC a matakin kasa. Amma sai a ka yi biris da su kamar ma ba su da wani gata a saman.

A na cikin haka ne fa, sai a ka ba Gawuna shugabancin hukumar gudanarwa ta jami’ar Bayero dake Kano, BUK. A na tafe kuma a ka kara masa da shugabancin hukumar gudanarwa ta Bankin bayar da lamunin gina gida, wato Mortgage Bank. A daidai kuma fa lokacin da a ka yi biris da Garo. Shi kansa Gawuna an yi korafin cewa ba haka ya kamata a yi masa ba, kasancewarsa dan takarar Gwamnan da ya fadi.

Advertisement

Amman fa duk da haka Gawuna ya fice daga jam’iyyar ta APC ya shiga ADC kwanan nan. Shi ma fa din neman makomar da ta fi dacewa da shi yake nema, ba dadi ba ragi. A hakan fa shi Garo bai fice daga APC ba bai kuma koma gefe ya na cin fuskar shugabanni ba.

Watakila daga cikin abubuwan da shugaba Tinubu ya kalla kenan har ya nemawa Garon waccan alfarma a wajen Gwamnan Kano din.

Advertisement

Ba kuma abinda ya ke ba ni mamaki sai zargin da a ke yi wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, wai ya na daga cikin masu kawo jinkirta lamarin ba wa Garo matsayin Mataimakin Gwamna. Ni dai a zancen gaskiya har yanzu ina tantamar wai a ce da sa hannun Sanata Barau. Musamman saboda ganin yadda nake tunanin akwai alaka mai kyau tsakaninsu.

Ni dai na san da cewa bayan da Sanata Barau ya gama wakilcinsa na dan majalisar tarayya daga Tarauni, a shekarun baya, lokacin Garo ya na shugaban karamar hukumar Kabo, shi Garo din ne ya yi wa Barau takardar shedar zama dan karamar hukumar Kabo. A matsayin Sanatan na cewa daga can ne dangin bangaren mahaifinsa yake.

Advertisement

Ko a lokacin cikin Ikon Allah sun dan shiryawa kansu cewar shi Barau din zai nemi takarar Gwamna, yayin da kuma Garo zai nemi Sanatan Kano ta Arewa. Amma kamar yadda Allah Ya shirya, Barau din ne ya samu tsayawa takarar Sanatan kuma ya ci. Ga shi nan kuma har kawo yanzu a na damawa da shi.

Sannan kuma Garo sau biyu ya na zama Babban Daraktan Kamfen na neman kujerar Sanata da Barau ya yi a shekarun 2015 da 2019. Hakan ya nuna maka cewar lallai akwai alaka mai kyau tsakanin wadannan muhimman mutane guda biyun. Shi ya sa da a ka ce Sanata Barau ya na daga yan gaba-gaba masu kawo cikas na tabbatar da Garo ya samu kujerar zama mataimakin gwamna sai nake jin abin gingirin a kaina.

Advertisement

Ni dai a ganina kuma a kashin gaskiya daga cikin duk wadanda a ka ce su na nema ko a na nema musu, ban ga wanda ya fi cancanta ba kamar Garo. In dai fa har za a cire son zuciya a lamarin. A ganina hakan na daga cikin dalilan da su ka sa har Shugaba Tinubu ke nema masa alfarma a wajen Gwamna.

Amman dai dabara ta rage ga mai shiga rijiya. Gaskiya ne cewar wannan dama ce da take a hannun Gwamna shi kadai. Amma fa faduwa da rashin ta a wasu lokuta mutum ne ke zabawa kansa a rayuwa.

Advertisement

Ni fa a ganina a hankalce tare da la’akari da alakar dake tsakanin Barau da Garo tun farko farkon dawowar wannan jamhuriyyar, Sanata Barau ba zai sauko kasa ya na yin hakan ba. Dan kuwa shi ma a kashin kansa ya san hakan ba dabara ba ce mai bullewa.

Ina kara kira ga Maigirma Gwamna Abba da ya kara mikewa tsaye ya sasanta tsakanin manyan APC. Ba wai tsakanin mutane biyu ko uku ko hudu ba, tsakanin su gaba daya. In ko Gwamna ya yi hakan da jagororin baya su ka kasa, to kuwa zai ginawa kansa gida a siyasar Kano. Kuma Kanon ba za ta taba mantawa da shi ba.

Advertisement

A siyasar Kano dole Barau ya na bukatar Garo. Haka shi ma Garo ya na bukatar Barau. Kamar yadda dukkan manyan ke bukatar junansu wajen samun nasarar tafiyar su ta siyasa.

Sai dai ko idan mutum ba zai ci gaba da siyasa ba, kawai zai je Saudiyya ne ko Sudan ko Egypt ko ya tattare a wajen Malaman soro ya kara samun ilimin addini, daga baya kuma Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya nada shi Limamin Masallacin Juma’ah. In ko ba haka ba, to dole kowa na bukatar kowa!

Advertisement

 

Anwar ya rubuto wannan ne daga Kano

Advertisement

Litinin, 6 ga watan Afrilu

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending