Connect with us

Opinion

Karfi Ya Kawo : Dubban Daruruwan Mutane Sun Tari Gwamna Abba

Published

on

IMG 20260406 WA0013

Daga Abba Anwar 

A ra’ayin wasu manazarta kan siyasar jihar Kano, sun fara tattauna cewar daga abubuwan dake faruwa kwanan nan alamu sun fara nuna cewar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, karfinsa a siyasa ya fara yin amo. Musamman daga lokacin da ya shiga cikin jam’iyyar APC.

Advertisement

An lura da cewar dama can akwai ayyuka tuli-tuli da yake yi ga jihar da al’ummar ta. Amma watakila babban abinda ya hana a gane hakan shine yadda a da din yake fuskantar mummunar adawa daga yan APC a lokacin. Saboda tsabar kwarewa a adawa har ta kai ba ma a ganin ayyukan Gwamna a lokacin.

Shugaban Kamaru Ya Naɗa Ɗansa A Matsayin Mataimakin Sa Kuma Shugaban Sojin Ƙasar

Advertisement

Amman fa daga lokacin da ya dawo cikin APC din da kuma dukkanin abubuwan da su ka biyo baya, da kuma kara samun yan midiya da soshiyal midiya da suke kara fito da ayyukan sa da tallata su, sai ya kasance an fara ma maganar ya fi wasu gwamnonin da su ka wuce na baya. Wajen wasu ayyukan ga jihar.

Wato irin cincirindon da a ka yi ranar Asabar lokacin dawowar sa daga Abuja bayan halartar taron jam’iyya na kasa da ya yi, na zaben shugabannin jam’iyyar, abin sai kawai wanda ya gani.

Advertisement

Wato tafiyar da take ba ta fi ta awa daya (1) ba kacal daga Airport zuwa Gidan Gwamnatin Kano, sai da ta dauke shi awanni bakwai (7). Wai a hakan ma an kakkaucewa wuraren da za su iya kawo mugun cunkoso.

Akalla an kiyasta jama’ar da su ka je taren Gwamnan sun kai dubban daruruwa. Kuma abin mamakin ma shine, ba fa wai yan jam’iyyar APC kawai ba ne. Akwai yan wasu jam’iyyun ma a taren da a ka yi masa.

Advertisement

Wasu da a ka yi hira da su sun nuna cewar su fa yan jam’iyyar ADC ne wasu kuma yan jam’iyyar PDP ne da ragowar wasu jam’iyyun ma. Kawai dai sun halarci taren Gwamnan ne saboda abubuwan alherin da ya yi a gwamnatin da su ka shafe su kai tsaye.

Akwai wadanda yan fansho ne. Wasu kuma iyalan yan fansho din ne. Sun ji dadin yadda Gwamnan ya tausayawa rayuwar su wajen ceto su daga kangin wahala ya biya musu kudaden da suke bin gwamnatin, tun daga gwamnatocin baya. Wasu ma da ba za su iya zuwa cikin cunkoson mutane ba, an gan su a kofar gidajen su suna dagawa Maigirma Gwamna hannu su na gaisuwa da jinjina gare shi.

Advertisement

Wasu kuma da yawa da a ka yi hira da su, sun ce sun fito ne daga gidajen su dan su yaba tare da jinjinawa Gwamnan ganin yadda ya tallafi rayuwar su a matsayin su na tsoffin kansiloli da kuma tsoffin masu ba wa shugabannin kananan hukumomi shawara a bangarori daban daban.

Wasu kuma sun fito ne saboda yadda Gwamnan ya dage wajen gyara hanyoyin da su ka shiga unguwanninsu da kuma ragowar titunan cikin birni. Da kuma kawata titunan.

Advertisement

Akwai wadanda kuma su ka ce sun fito ne saboda su nuna goyon bayan su ga manufofin alheri da cigaba na gwamnatin Abban.

A takaice dai abin da a ke so a nunawa mai karatu shine, dubunnan daruruwan jama’ar da su ka fito ba wai tsantsagwaron yan APC masoya Abba ba ne kawai. Har ma da akwai mutanen gari wadanda ba ma ruwan su da siyasa. Kawai sun ce ya cancanta tun yanzu su fara nuna masa goyon baya kafin ma lokacin zabe ya zo.

Advertisement

Ya rage ga Maigirma Gwamna ya ci gaba da yin ayyukan alherin da su ka jawo masa irin wannan farinjini. An ce dai dama Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba a ke gane ta.

Sannan babban abin ban sha’awa shine yadda a ka ga fuskokin wasu daga cikin jagororin yan tsohuwar APC, wadanda ke cikin jam’iyyar kafin shigowar Gwamnan. Misali an ga tsohon shugaban jam’iyyar na Kano, Dan Sarki Abdullahi Abbas. An ga Sanata Kawu Sumaila, an hango mutane irin su Malam Nasir Bala Ja’oji.

Advertisement

Haka nan an hango gungun mutanen Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na Kasa, Sanata Barau Jibrin. Da na dandazon mutanen Hon Murtala Sule Garo. Da kuma da yawa daga cikin jagororin tafiyar APC a Kano.

Akwai mutanen da Gwamnan ya shigo APC da su wadanda sun taka rawar gani wajen wannan gagarumar tarba da a ka yi wa Gwamnan. Irin su shugabar ALGON, shugabar karamar hukumar Tudunwada, Hajiya Sa’adatu, da shugabannin kananan hukumomin Nassarawa, Gwale, Kabo, da na Dawakin Tofa. Wato Yusuf Imam (Ogan Boye), Abdullahi Muazu (Mojo), Lawan Najume da kuma Anas Danmaliki

Advertisement

Daga cikin Kwamishinoni kuma ba za a iya kau da kai daga kokarin da irin su Kwamishinan Kasa da Safiyo, Abdujabbar Garko da Kwamishinan Muhalli, Dr Dahiru Hashim su ka yi ba. Wadannan mutanen sun yi da jikin su lokacin taren Gwamnan.

Sannan an ga gungun jama’ar Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi da Ma’aikatar Ilimi Mai Zurfi, Ali Haruna Makoda, duk da cewar a lokacin bai samu dawowa daga Kasa Mai Tsarki ba. Amma an ga jama’arsa dodo-dodo. Wato masu yi dan Allah kenan. Akramakallah

Advertisement

Anwar ya rubuto daga Kano, 

Litinin, 6 ga watan Afrilu, 2026

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending