News
An Hallaka Ɗalibi A Bikin Sabbin Ɗalibai A Jami’ar Neja
Wani ɗalibi mai shekara 25 da ke aji uku a Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Kontagora a Jihar Neja, Seyi Simon, ya riga mu gidan gaskiya bayan an daɓa masa wuƙa a yayin wani biki da aka shirya wa sabbin ɗalibai.
Aminiya ta ruwaito cewa Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren Litinin a ɗakin taro na jami’ar, inda aka ce rikici ya ɓarke tsakanin mamacin da wani matashi mai shekaru 18, Jafar Musa.
An Kama Mutane Biyar Da Ake Zargi Da Hannu A Harbin Wata Budurwa A Maiduguri
Majiyoyi sun ce rikicin ya samo asali ne daga saɓani da ya fara da muhawara, kafin daga bisani ya rikiɗe zuwa faɗa, inda ake zargin wanda ake tuhuma ya daɓa masa wuƙa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an garzaya da wanda aka caka wa wuƙar zuwa Asibitin Ƙontagora, inda a nan aka tabbatar da rasuwarsa.
Ya ƙara da cewa an kama wanda ake zargi, kuma ana ci gaba da bincike domin gano cikakken abin da ya faru.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
