News
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban K/H Tarauni Kan Rikicin Sabunta Kasuwar Gyadi-Gyadi Yar Kasuwa
DAGA MUSA ADO MUSA
Wani mazaunin karamar hukumar Tarauni a Jihar Kano, Musa Ado Musa, ya rubuta budaddiyar wasika ga shugaban karamar hukumar, Hon. Ahmad Sekure, inda ya bukaci a sake duba yadda ake aiwatar da shirin sabunta kasuwar ‘Yar Kasuwa da ke unguwar Gyadi-Gyadi.
A cikin wasikar, marubucin ya bayyana cewa duk da cewa yunkurin sabunta kasuwar abu ne mai kyau da zai kawo ci gaba, akwai bukatar a gudanar da shi cikin tsari mai kyau da adalci domin kaucewa tauye hakkin masu shaguna da kuma matasan da ke cin moriya daga kasuwar.
An Hallaka Ɗalibi A Bikin Sabbin Ɗalibai A Jami’ar Neja
Ya ce daya daga cikin manyan matsalolin da ke kunno kai shi ne rashin cikakken hadin kai tsakanin shugabannin kasuwar, lamarin da ya haifar da rabuwar kai tsakanin masu goyon bayan aikin da kuma masu adawa da shi. A cewarsa, hakan na faruwa ne sakamakon rashin isasshen bayani kan makomar mallakar shagunan bayan kammala aikin.
Haka kuma, ya koka kan rashin wata sahihiyar takardar yarjejeniya tsakanin karamar hukumar da masu shaguna, inda ya ce da dama daga cikinsu ba su san yadda tsarin zai kasance ba, ballantana su san kamfanin da zai aiwatar da aikin.
Musa Ado Musa ya kuma zargi wasu wakilai da ake cewa suna tattaunawa da masu shaguna da yi musu barazanar cewa za a kwace shagunan duk wanda ya ki amincewa da tsarin da ake son aiwatarwa.
Bugu da kari, ya nuna damuwa kan yadda ake zargin wasu na wakiltar masu shaguna ba tare da cikakken yardar kowa ba, yana mai cewa ya dace duk masu ruwa da tsaki su samu bayanai a sarari domin tabbatar da gaskiya da adalci.
Dangane da rayuwar al’umma, marubucin ya jaddada cewa sama da matasa 1,000 ne ke dogaro da kasuwar wajen neman abinci, yana mai cewa wajibi ne a yi la’akari da makomarsu kafin daukar kowane mataki.
A karshe, ya yi kira ga shugaban karamar hukumar da ya tabbatar da cewa an yi nazari mai zurfi tare da fifita maslahar al’umma gaba daya, yana mai cewa dorewar shugabanci na samuwa ne idan aka tabbatar da adalci da gaskiya.
Ya kuma bukaci a bude tattaunawa da masu ruwa da tsaki domin samar da mafita mai dorewa akan wannan batu.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
