News
KANO: Wasu Bata Gari Sun Sarewa Wani Mai Mukamin Gargajiya Hannu Yayin Kai Dauki
A Jihar Kano, wasu da ake zargin ‘yan fashin babur ne sun sare wa wani malami hannu a Karamar Hukumar Bunkure, yayin da yake kokarin kai dauki ga wani da ake yi wa fashi.
Lamarin na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran Masarautar Rano, Nasiru Habu Faragai, ya fitar a ranar Laraba, 8 ga Afrilu 2026.
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargadi Game Da Yiwuwar Fuskantar Ambaliyar Ruwa A Jihohi 10
Sanarwar ta bayyana cewa, malamin mai suna Isah Sallama na Sarkin Bakar Rano ya gamu da wannan mummunan hari ne a lokacin da ya yi kokarin taimakawa wani Malam Sauwanu Hadi, wanda wasu da ba a san ko su waye ba suka yi yunkurin kwace masa babur da wayar hannu.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne da dare a hanyar Funkuyi, karkashin Dagacin Buran. A cewar sanarwar, maharan sun yi yunkurin harbe Isah Sallama, amma bindigar ba ta yi aiki ba, kafin daga bisani su sare masa hannu, lamarin da ya sa aka bar shi cikin mawuyacin hali.
Hakimin Bunkure, Alhaji Aminu Isa Umaru, ne ya gabatar da rahoton faruwar lamarin a gaban Sarkin Rano, Ambasada Muhammad Isa Umaru.
Bayan faruwar lamarin, Sarkin Rano ya bayar da tallafin naira dubu dari ga wanda abin ya shafa domin taimakawa wajen kula da lafiyarsa, tare da umartar a mika batun ga jami’an ‘yan sanda domin gudanar da bincike.
Haka kuma, Sarkin ya yi kira ga shugabannin yankuna da jami’an tsaro da su kara kaimi wajen dakile ayyukan ‘yan fashi da sauran masu aikata laifuka a yankin.
