Connect with us

Opinion

Kujerar Mataimakin Gwamna : Jaddada Matsayata Da Kalubalantar MUNAFUKAI

Published

on

1776584732758

Daga Abba Anwar 

Ba wai maganar Mubahala ba, dan a waje na wannan abin ba shi da wannan matsayin a rayuwata. Duk da haka zan ce, IDAN AKWAI WANDA YA SAN WANI YA BA NI WANI ABU DAN NA YI WANI RUBUTU NA BATANCI, NA BA WA ABOKAN ADAWAR WANI KO WASU BA TARE DA AN SA SUNANA BA, A KAN WANNAN DAMBARWA TA NEMAN MATAIMAKIN GWAMNA A KANO, MUTUM KUMA YA YI SHIRU BAI FITO YA TONA BA TARE DA KWARARAN HUJJOJI, ALLAH YA TSINE MASA! IDAN KUMA NI DIN NA SAN WANI YA BA NI WANI ABU DAN NA YI WANI RUBUTU NA BATANCI NA BA ABOKAN ADAWAR WANI KO WASU NA CE SU YI AMFANI DA RUBUTUN AMMA KAR SU SA SUNANA, YANZU KUMA NA CE BA A YI HAKA BA, TO ALLAH YA TSINE MIN!! IDAN KUMA AKWAI WANI KO WASU DA SUKA TABA BA NI WANI ABU SU KA CE NA YI RUBUTUN BATANCI NA BA SU, SU SA WANI SUNA BA NAWA BA, SU KA YADA, YANZU KUMA SU KA YI SHIRU BA SU FITO SUN FADA BA, TO SU MA ALLAH YA TSINE MUSU!!!

Advertisement

Ni fa a waje dukkan masu neman kujerar mataimakin gwamnan jihar Kano su na da dama a siyasance na yin hakan. Dukkansu su na da kima a ido na. Ban ga abin zagi ba dan an ce ga wani ya na son kujerar da ni ba shi nake da sha’awar a ba ba. Saboda haka ba wani abin tayar da jijiyar wuya wajen kowa ya nuna kwadayinsa a fili kan wannan bukata, da ma duk wata bukata ta siyasa.

A wani rubutu na da na yi kwanan nan mai taken “Why Hues, Cries Against Garo?” wanda na yi ranar 5 ga watan Afrilu, 2026, na fadi ra’ayi na cewar ni fa a waje na, Murtala Sule Garo ne ya fi cancanta.

Advertisement

Daga cikin dalilan da na bayyana, akwai maganar cewar bayan an fadi zaben gwamna na 2023, wanda ya yi takarar mataimakin Dr Nasiru Yusuf Gawuna, daga shi har Gawuna ba a kula da ba wa kowannensu mukami a gwamnatin tarayya ba. Sai daga baya a ka ba Gawuna wasu mukamai. Amma Garo a ka ci gaba da yin watsi da shi ba tare da an ba shi wani mukami ba.

An Kama Dalibai 2 Da Wasu Iyaye Kan Zargin Kirkirar Makin Jarrabawar JAMB

Advertisement

Daga baya kuma Gawuna ya fice daga APC din zuwa ADC. Dan neman mafita ta sosai a siyasance. Wanda ban ga laifin sa ba. Shi kuma Garo duk da ba a ba shi mukamin komai ba, amma ya ci gaba da zama a jam’iyyar. Tare kuma da cigaba da tallafawa yan jam’iyyar ba dare ba rana. A dalilin haka na ce wannan damar da a ka samu ta mataimakin gwamna ta fi dacewa da shi kai tsaye.

Ni dai, ba kuma tare da alfahari ba, idan ina da wani ra’ayi ko wata fahimta ta siyasa ban iya boyewa ba. Ba na iya zuwa nan in ce wani abu sannan in je can in ce wani abu daban. Akwai lokacin da a ka yi zaben maye gurbi kwanakin baya can na ‘yan majalisar Tsanyawa/Kunchi da kuma Bagwai/Shanono, na san a lokacin sakamakon da hukumar zabe ta fitar bai wa wasu yan jam’iyyar APC dadi ba.

Advertisement

A nan ne fa na yi wani rubutu ina kalubalantar wadanda ke rike da mukaman gwamnatin tarayya da su ka fito daga bangaren, wato Kano ta Arewa. A wani rubutu na da na yi mai taken, “Kano By-election : The Beginning of an End Era,” ranar 17 ga watan Agusta, 2025, bayan na kalubalanci masu rike da makamai daga bangaren, na shawarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, da ya sauke duk ire-iren masu mukaman da ya nada marasa amfani. Da na tashi bayar da misali, ai sunan dan tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje na kama, wato Abba Ganduje, na ce ya kamata Tinubu ya cire irin sa daga mukami.

Na kawo wannan misalin ne dan na nunawa mai karatu cewar, ni ban iya munafuncin boye abu ba, kuma in je wani wuri ina zagin wani. Ka ga dai ai Abba Ganduje dan Megidana ne da na taba yi wa aikin babban sakataren yada labarai, na tsahon shekaru 6, lokacin ya na gwamnan Kano. A lokacin da na ji ma a na fadin cewar ya na ta fadin maganganu, shi Abban, ai cewa na yi ma a gaya masa, ba ma a nan kawai zan tsaya ba, duk lokacin da ya fito takara ko ta mecece, duk da ba mazabarmu daya ba, har can zan je kuma na yaki bukatar tasa ta siyasa.

Advertisement

Ni ban iya boye ra’ayina ba. Balle wai har na je na yi rubutu na batanci ga wani in ba abokan adawarsa in ce su sa amma kar su sa sunana. Ko da na yi rubutun nan da na kawo misalin Abba Ganduje, ai sunana na sa. Na bayar a ka buga a jaridu. Kuma na yada su da kaina ba wani dan aike.

Dukkan wadanda ke neman samun wannan mukamin na mataimakin gwamna a Kano, su na da girma da mutunci a ido na. Kai ba ma su ba, ina yaron nan da a ke kira da Maituta, wanda yake shiga gaban tawagar gwamna ya na wasa da mashin da tutocin jam’iyya a hannunsa, to wallahi ya na da kima a idona.

Advertisement

Wadannan masu neman wannan kujera sune tsohon kakakin majalisar dokoki ta jihar, Kabiru Alasan Rurum, da tsohon sakataren gwamnatin jihar, Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi da kakakin majalisar dokokin jihar na yanzu, Jibrin Ismaila Falgore, da tsohon dan takarar mataimakin gwamna a zaben 2023, Murtala Sule Garo. Wadannan sune wadanda ‘yan tsohuwar APC su ka bayar ga Maigirma Gwamna, Abba Kabir Yusuf, idan ka cire kakakin majalisa Falgore. Wanda shi ba dan tsohuwar APC ba ne. Tare da gwamnan su ka shigo APC din.

Amman abinda na lura da shi shine, a tare da wasu daga cikin masu neman wannan kujera, akwai wasu mutane masu fakewa da soyayya su na kara gurbata tsakanin mutane da wadannan shugabanni. Kuma saboda rashin kwarewa ta rayuwa, su na kara jawowa jagororin nasu makiya.

Advertisement

Ni fa a waje na, mutum ba makiyi ba ne dan ya na neman wani matsayi da nake ganin ba shine ya fi cancanta da matsayin ba. Ai ita siyasa fa gaba dayan ta bukata ce. Akwai bukatar kai, akwai bukatar al’umma, sannan akwai wadanda su ka hade bukatar kai din da ta al’umma waje daya.

Kasancewar na fi yi wa matamakin shugaban majalisar dattawa na kasa, Sanata Barau Jibrin, CFR, rubuce – rubuce a wannan zubin siyasar da muke ciki, hakan ba kuma ya na nufin ba zan iya yabon Garo ba. A waje na ba laifi ba ne, idan na ce ni Garo nake ganin ya fi cancanta da wannan kujerar ta mataimakin gwamna.

Advertisement

A baya ai na sha yin rubutu ina dora laifin tabarbarewar harkokin jam’iyyar APC a Kano, a kan shugabanci da kuma dattawan jam’iyyar. Tun ma kafin gwamna Abba ya shigo da kuma har lokacin da ya shigo din. Misali akwai rubutun da na yi mai taken, “Kano APC in Discombobulation : As Ploys Against DSP Barau Thickens,” ranar 15 ga watan Disamba, 2025. Ban boye sunana ba a rubutun. Kuma ban ba wani na ce ya sa sunan kowa ba. Da ban yi haka ba sai yanzu ne zan yi hakan.

Wani abinda mai karatu bai sani ba shine, duk lokacin da na yi wani rubutu a kan Barau, wato Garo ya na daga cikin mutane ma farko da nake turawa “links” idan an buga a jaridu. Kuma bai taba canza min fuska ba. Bai taba ce min dan me ya sa na yi haka ba.

Advertisement

Shi ma Barau duk wani rubutu da na yi na yabi Garo, sai na tura masa. Kuma wallahi bai taba nuna min bacin ransa ba. Kuma bai taba ce min dan me na yi haka ba. Ni fa ban yarda wai dan ina tare da wane in dinga zagin wane ba kuma. Yin hakan rashin sanin rayuwa ne. Gidadanci ne da jahilci da toshewar basira.

Babban jan hankali na ga masu kara dagula al’amuran APC a jihar Kano shine, ya kamata su fahimci cewar, muddin fa a haka, a ta-ci-barkatai za a ci gaba da tafiya, to tabbas gwamna Abba zai yi wa ‘yan tsohuwar APC abinda ya ga dama. Kuma wallahi ba abinda wani ya iya. Za a zo lokacin da yanayi zai nunawa kowa cewar, gwamna Abba ya zama Liman dole a bi shi. Ko a canza masallaci.

Advertisement

Shi fa Maigirma gwamna, a wajen sa in dai ka na da sama, to kujerar ka tamkar ta samu ne ko ka ci zabe ko ba ka ci zabe ba. Kuma ba wanda ya isa ya cire shi daga wannan tunanin. Dan kuwa ta faru a kansa a zaben 2019. Sannan a zaben 2023 kuma babbar matsalar daga cikin da’irar APC din a ka samu akasi. A ka nunawa Gawuna da Garo kyashi da bakinciki da kuma tsagwaron mugunta. Kuma daga cikin APC din.

Ni kullum a rubuce-rubuce na kira nake yi na ya zama dole a samu hadin kai tsakanin ‘yan tsohuwar APC. Daga shugabanninsu zuwa ga mabiyansu. Ka bi duk rubuce – rubuce na daya bayan daya za ka ga babban burina shine samun hadin kan ‘yan jam’iyya.

Advertisement

Shi fa gwamna Abba yanzu a wajen sa watakila ya na da tunanin ba ya bukatar hobbasar kowane dan tsohuwar APC. Kun dai ga yadda a ka tara masa dubunnan mutane lokacin da ya dawo daga Abuja kwanan baya. Kuma fa a daidai lokacin da shugabannin tsohuwar APC ke ta yakar juna. Abu ne mai sauki ga gwamna ya yi watsi da kowa dan tsohuwar APC, ya shiga harkar gabansa.

Ina kara jaddada kira ga jagororin tsohuwar APC cewar hadin kai fa ya zama dole. Kowa na bukatar kowa. Ko sun yarda ko ba su yarda ba. Tafiya a rarrabe tsakaninsu na iya kawo bullar wani yanayi na wa-ka-ci-ka-tashi a zaben cikin gida da yake fuskantar duk jam’iyyu. Kasancewar kakar zabe ta matso.

Advertisement

 

Anwar ne ya rubuta daga Kano

Advertisement

Lahadi, 19 ga watan Afrilu, 2026

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending