News
Farfesa Abdalla Uba Adamu Ya Yi Ritaya Daga Jami’ar Bayero Kano Bayan Shekaru 46 Na Aiki
Tsohon Shugaban karatu daga gida na National Open University of Nigeria, Farfesa Abdalla Uba Adamu, ya sanar da yin ritaya daga aiki a Jami’ar Bayero ta Kano bayan ya kai shekaru 70 a duniya.
Farfesan ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook a daren Juma’a, inda ya kawo ƙarshen kusan shekaru 46 da ya shafe yana koyarwa da gudanar da bincike a jami’ar.
Rashin Kula Da Masu Buƙata Ta Musamman Ne Ke Janyo Yawaitar Mabarata A Arewacin Najeriya —Ganduje
A cewarsa, ya fara aiki ne a ranar 24 ga watan Yuli, 1980 a matsayin mataimakin malami a sashen Ilimi, kafin daga bisani ya kammala aikinsa a sashen nazarin watsa labarai da sadarwa—wani fanni da ya taka rawa wajen kafuwarsa a shekarar 2014.
Farfesa Adamu, wanda ke koyarwa a fannonin Ilimin Kimiyya da kuma Sadarwa da Al’adu, ya ce rayuwarsa ta ilimi ta kasance mai cike da ƙalubale da nasarori, yana mai cewa bai yi nadamar zaɓin wannan fanni ba.
Ya kuma bayyana cewa a farko ya yi tunanin karantar likitanci bayan tattaunawa da mahaifinsa, amma daga bisani ya karkata zuwa fannin bincike da ilimi wanda ya fi dacewa da sha’awarsa.
Farfesan ya gode wa iyalansa da abokan aiki bisa goyon baya da suka ba shi tsawon shekarun aikinsa.
Sai dai ya jaddada cewa ritaya ba ƙarshen aiki ba ne, domin zai ci gaba da gudanar da bincike da rubuce-rubuce, tare da shirin kammala wasu littattafai da yake aiki a kansu.
