Connect with us

News

Dogon Jira A Asibitocin Gwamnati Na Ci gaba da Jefa Marasa Lafiya cikin Wahala A Najeriya

Published

on

Doctors stretched thin due to brain drain 768x547

Marasa lafiya na ci gaba da fuskantar matsananciyar wahala a asibitocin gwamnati, inda suke shafe dogon lokaci kafin samun damar ganin likita a Najeriya

Binciken da Jaridar Daily Trust suka gudanar ya nuna cewa a manyan biranen Abuja, Kano, Rivers State da Lagos, marasa lafiya kan jira tsakanin sa’o’i biyar zuwa bakwai kafin a kula da su. A wasu lokutan, hakan na sa su rasa aikinsu na yini baki ɗaya.

Advertisement

Dogon Jira A Asibitocin Gwamnati na Ci gaba da Jefa Marasa Lafiya cikin Wahala A Najeriya

A yankunan karkara kuwa, lamarin ya fi tsanani, inda ake samun jinkirin da kan kai har kwanaki, sakamakon ƙarancin likitoci da kuma raunin cibiyoyin kiwon lafiya.

Advertisement

Masana sun danganta wannan matsala da ƙarancin ma’aikatan lafiya, da kuma yawaitar likitocin da ke ficewa zuwa ƙasashen waje domin neman ingantacciyar rayuwa.

Rahotanni daga Nigerian Association of Resident Doctors sun nuna cewa dubban likitoci sun bar ƙasar cikin shekaru goma da suka gabata. A halin yanzu, yawan likitoci bai kai ƙa’idar World Health Organization ba, wadda ta tanadi mafi ƙarancin likitoci 10 ga mutane 10,000.

Advertisement

Ƙungiyoyin likitoci sun dade suna koka kan rashin kyawun yanayin aiki da ƙarancin albashi, waɗanda ke ƙara ingiza kwararru barin ƙasar.

A Asibitin Kubwa da ke Abuja, marasa lafiya na cika wuraren jira tun da sassafe. Wasu na zuwa tun ƙarfe 6:00 na safe, amma su kan jira har zuwa rana kafin ganin likita.

Advertisement

“Na zo da sassafe, amma har tsakar rana ba mu ga likita ba,” in ji wata uwa, Grace Folusho.

Haka lamarin yake a Murtala Muhammed Specialist Hospital, inda marasa lafiya ke shafe awanni masu yawa a layi, wasu ma ana tura su su dawo washegari.

Advertisement

A Aminu Kano Teaching Hospital ma, karancin likitoci na ƙara tsananta matsalar, duk da yawan marasa lafiya da ke zuwa kullum.

A nata bangaren, Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya ta ce tana kokarin shawo kan matsalar ta hanyar bullo da manufofi da za su rage yawan likitocin da ke barin ƙasar, tare da inganta tsarin kiwon lafiya.

Advertisement

Sai dai masana na ganin cewa har sai an ƙara zuba jari sosai a bangaren lafiya, musamman a cibiyoyin matakin farko, matsalar za ta ci gaba da addabar marasa lafiya a faɗin ƙasar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending