News
Dakarun Sojin Sun Hallaka Jagororin ‘Yan Bindiga Anaruwa Da Gomina Da Wasu 7 A Zamfara
Dakarun rundunar sojin Nijeriya, sun kashe wasu manyan jagororin ‘yan bindiga biyu—Anaruwa da Gomina—tare da wasu mutum bakwai a jerin hare-haren da aka gudanar cikin kwanaki uku a jihohin Zamfara da Katsina.
Mataimakin Daraktan Yaɗa Labarai na rundunar, Sashe na 8 da Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa.Ya bayyana cewa a Jihar Zamfara, dakaru daga sansanin gaba-gaba da ke Bagega sun kai wani farmaki mai haɗari a ƙaramar hukumar Anka, wanda ya kai ga kashe ‘yan ta’adda bakwai, ciki har da shahararrun jagorori Anaruwa da Gomina.
An Rantsar Da Murtala Sule Garo A Matsayin Sabon Mataimakin Gwamna Kano
An kuma bayyana cewa Anaruwa ƙanin shahararren jagoran ‘yan bindiga ne, Kachalla Idi Aiki.
Laftanar Kanal Olaniyi ya ƙara da cewa a farkon farmakin, dakarun sun yi arangama da ‘yan ta’addan a kan hanyar Bagega zuwa Anka, inda aka yi musayar wuta mai tsanani tsakanin ɓangarorin biyu.
