Connect with us

News

Kotu Ta Daure Wani Limamin Masallacin Juma’a Wata 1 Kan Tura Bidiyon Tsaraici Ga Matar Aure A Kano

Published

on

Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola, ta yanke wa wani limamin Juma’a hukuncin ɗaurin wata ɗaya ba tare da zaɓin tara ba, bayan samunsa da laifin tura bidiyon tsaraicinsa ga matar aure ta hanyar WhatsApp.

Freedom Radio ta ruwaito cewa limamin, wanda kuma mai kula da wata makaranta ne a Abuja, ya shiga hannu ne bayan mijin matar ya kai ƙorafi ga jami’an ‘yan sanda, inda ya zarge shi da neman matarsa tsawon kusan shekara guda.

Advertisement

Cutar Sanƙarau Ta Hallaka Yara 33 A  Sakkwato 

Rahotanni sun nuna cewa wanda aka yankewa hukuncin ya riƙa tura wa matar bidiyoyin tsaraicinsa duk da cewa ta shaida masa tana da aure.

Advertisement

Sai dai duk da hakan, limamin ya ci gaba da matsa mata lamba tare da rokonta da ta amince da buƙatarsa, yana mai cewa bai yarda tana da aure ba.

Bayan gurfanar da shi a gaban kotu da kuma karanta masa tuhume-tuhumen da ake yi masa, ya amsa laifin tare da roƙon kotun ta sassauta masa hukunci.

Advertisement

Daga bisani, Mai Shari’a Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya yanke masa hukuncin ɗaurin wata guda ba tare da zaɓin tara ba, domin zama darasi ga masu aikata irin wannan ɗabi’a.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending