News
Gwamnatin Shugaba Tinubu Za Ta Kashe Dala Biliyan 11.6 Wajen Biyan Kudin Ruwan Basussukan A 2026
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Najeriya za ta kashe kimanin dala biliyan 11.6 wajen biyan kuɗaɗen ruwa da sauran basussukan da ake bin ƙasar a shekarar 2026.
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da yake jawabi a taron Africa Forward Summit da aka gudanar a cibiyar taruka ta Kenyatta Convention Centre da ke Nairobi, babban birnin ƙasar Kenya.
Kotu Ta Aike Da Tsohon Ministan Lantarki, Saleh Mamman Gidan Yari Na Shekaru 75
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya ce adadin kuɗin da za a kashe wajen biyan bashin ya kai kusan rabin kuɗaɗen shiga da gwamnatin tarayya ke sa ran samu a shekarar.
Tinubu ya kuma bayyana cewa duk da ƙoƙarin da Najeriya ke yi wajen gyara tsarin kuɗinta, cibiyoyin bayar da lamuni da hukumomin ƙididdigar kuɗi na duniya na ci gaba da kallon ƙasashen Afirka a matsayin masu haɗarin bashi.
A cewarsa, hakan na sa ƙasashen nahiyar ke karɓar lamuni da Kudin ruwa mai yawa idan aka kwatanta da ƙasashen Turai, Asiya da Arewacin Amurka.
Shugaban ya ce hakan na kawo cikas ga burin gina haɗin gwiwar masana’antu tsakanin ƙasashen Afirka ƙarƙashin yarjejeniyar cinikayya ta bai ɗaya ta Afirka (AfCFTA).
Sai dai Tinubu ya ce gwamnatin sa ta samu nasarar farfaɗo da ɓangaren bankunan Najeriya, inda ya ce jarin bankunan ƙasar yanzu ya zarce dala biliyan 3.4.
Ya kuma ce hakan ya taimaka wajen fitar da Najeriya daga jerin ƙasashen da hukumar FATF ke sanya ido a kansu kan zargin matsalolin hada-hadar kuɗi.
