Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Kama Tabar Wiwi Ta Kimanin Naira Biliyan 10 A Legas

Published

on

images (2)

Hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Najeriya ta kama tabar wiwi ta kimanin naira biliyan 10 da rabi a jihar Lagos bayan an shigo da ita daga ƙasar Canada.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi ya fitar a yau Laraba tare da aike wa RFI Hausa.

Advertisement

Gwamnatin Shugaba Tinubu Za Ta Kashe Dala Biliyan 11.6 Wajen Biyan Kudin Ruwan Basussukan A 2026

Sanarwar ta ce jami’an NDLEA ne suka samu nasarar ƙwace tabar mai nauyin kilogram dubu 4,173 da darajarta ta kai biyoyin naira a tashar ruwan Tincan da ke jihar Lagos.

Advertisement

 

Kamen miyagun ƙwayoyin ya biyo bayan tattara bayanan sirri, da bibiya tare da bincike da hukumomin su ka yi.

Advertisement

Fiye da watanni biyu aka shafe ana binciken haɗin gwiwa tsakanin NDLEA da hukumar kula da tashar ruwan Tincan, da hukumomi na ƙasa da ƙasa, musamman daga Amurka da Birtaniya da kuma jami’an Canada.

Wannan na zuwa ne kwanaki guda bayan NDLEA ta kama wasu ƙwayoyi da darajarsu ta kai naira biliyan biyar da miliyan 815.

Advertisement

 

 

Advertisement

RFI

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending