Connect with us

News

Idan An Matsa Mana, Za Mu Bude Baki Mu Yi Magana ‎ ‎— Martanin Gwamna Abba Kabir Yusuf Ga Kwankwaso

Published

on

Mun daina rusau sai dai mu kai mutum kurkurku kai tsaye Gwamnatin Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi tsohon ubangidansa na siyasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ya ja girmansa ko kuma ya soma mayar masa da martani.

‎Gwamnan ya bayyana cewa kada a ɗauki shirun da yake yi a matsayin tsoro, la’akari da abin da ya kira rashin jan girma saboda ci gaba da furta kalamai marasa daɗi da tsohon gwamnan yake yi a kansa.

Advertisement

Mutane Da Dama Sun Jikkata Yayin Da Mota Ta Murkushe Adaidaita Sahu ‎

‎Wannan ne karo na farko da Gwamna Abba Kabir ya fito fili yana mayar wa Kwankwaso martani tun bayan raba gari da suka yi a siyasance a farkon wannan shekara.

Advertisement

‎A yayin wata hira da Kwankwason ya yi a bayan nan tare da Gidan Talabijin na TrustTV, ya goranta wa Gwamna Abba dangane da abin da ya bayyana cewa shi ya yi masa duk wata suturu a siyasance har ya zama gwamna.

‎A yayin hirar ce kuma Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir zai ciji yatsa kan abin da ya kira babban kuskure saboda hannun riga da ya yi da shi.

Advertisement

‎Sai dai a yayin taron tabbatar da Sulaiman Kawu Sumaila a matsayin ɗan takarar sanatan Kano ta Kudu a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC a Rano, Abba ya ce idan tura ta kai bango zai fara mayar da martani.

‎“Shirun da muke yi ba fa tsoro ba ne. Ina dalilin da mutum mai shekara 69 zai riƙa kiran mai shekara 63 a matsayin yaro saboda kawai ya girme shi kaɗan,” in ji shi.

Advertisement

‎Gwamnan ya ƙara da cewa idan dattijo bai mutunta kansa ba, to matashi ma zai sami abin faɗi, yana mai roƙon ’yan Kwankwasiyya da su daina furta kalaman da za su iya jawo tonan asiri.

Advertisement

Advertisement

Aminya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending