News
Yan Bindiga Sun Yi Fashin Ragunan Layya A Kano
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun yi wa wasu ’yan kasuwar raguna daga Karamar Hukumar Ajingi ta Jihar Kano fashi, inda suka kwace musu raguna 11 yayin da suke hanyarsu ta zuwa Jihar Kogi domin gudanar da cinikin Babbar Sallah.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne cikin dare a garin Dakatsalle da ke Karamar Hukumar Bebeji, lokacin da ’yan kasuwar suka tsaya jiran motar da za ta dauke su zuwa garin Ankpa da ke Jihar Kogi.
Yansanda Sun Cafke Mutane 248 Da Ake Zargi Da Laifuka A Kano
Arewa Updates ta rawaito cewa, maharan sun iso cikin wata mota dauke da bindigu, inda suka rika harbin iska domin firgita mutane kafin su aiwatar da fashin.
Daya daga cikin wadanda abin ya shafa, Alhaji Hamisu Abdu Sakalawa, ya bayyana cewa maharan sun umurce su da su kwanta tare da rufe idanunsu bayan sun yi harbe-harbe a iska.
“Sun zo ne cikin mota dauke da bindigu, suka fara harbin iska sannan suka umurce mu da mu kwanta kasa tare da rufe idanunmu. Daga nan suka kwashe ragunanmu guda 11 suka gudu,” in ji shi.
Ya kara da cewa bayan faruwar lamarin, sun kai rahoto ofishin ’yan sanda na Dakatsalle domin daukar matakin da ya dace.
Lamarin dai ya haddasa fargaba a tsakanin ’yan kasuwar dabbobi, musamman a daidai lokacin da ake shirye-shiryen cinikin Babbar Sallah a fadin kasar nan.
