Connect with us

News

Zan Dauki Matakin Shari’a A Kan Duk Wanda Ya Kara Cewa Ina Bai Wa ‘Yan bindiga Kariya —Sheikh Gumi

Published

on

Sheikh Gumi 750x430 (2)

Fitaccen malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya bayyana cewa ba shi da wata alaƙa da duk wasu bayanai ko bidiyoyi da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta da ke nuna kamar yana goyon bayan ayyukan ’yan bindiga.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai ranar Asabar, Sheikh Gumi ya ce wasu mutane masu ra’ayin ƙabilanci da son zuciya suna amfani da wasu hirarrakinsa da ya yi kan matsalar tsaro wajen karkatar da maganganunsa domin yaudarar jama’a.

Advertisement

Jami’an Yansanda Sun Kama Matashi Kan Kashe Kakansa Da Wuka

Ya ce wasu masu amfani da kafafen intanet suna yanke sassan jawabansa ko hirarrakinsa tare da sauya ma’anarsu domin neman jan hankali da samun karɓuwa a shafukan sada zumunta.

Advertisement

“Ina sanar da jama’a cewa duk wani bidiyo, rubutu ko saƙo da ake danganta mini da goyon baya ko kare ayyukan ’yan bindiga, ba daga gare ni ya fito ba,” in ji Gumi.

Malamin ya jaddada cewa bai taɓa goyon bayan ayyukan ta’addanci ko ’yan bindiga a ko’ina cikin Najeriya ba, yana mai cewa kullum yana kira ne ga samar da hanyoyin kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin lumana da adalci.

Advertisement

Sheikh Gumi ya kuma yi kira ga jama’a, kafafen yaɗa labarai da hukumomin gwamnati da su yi watsi da duk wani bayani na ƙarya da ake yaɗawa da sunansa.

 

Advertisement

 

NAN

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending