Connect with us

News

2027: Ba Zan Taba Juya Wa Kwankwaso Baya Ba — Goro

Published

on

IMG 20260527 WA0009

Dan takarar kujerar majalisar wakilai ta tarayya na mazabar Fagge karkashin jam’iyyar NDC a zaben 2027, Sulaiman Goro, ya bayyana cewa babu wani lokaci da zai taba rabuwa da jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, yana mai cewa biyayyarsa ga tafiyar ta samo asali ne daga akida ba wai siyasar anfani ba.

Tsohon dan majalisar wakilan, wanda ya taba wakiltar mazabar Fagge tare da jagorantar kwamitin kula da manyan makarantu na majalisar wakilai, ya bayyana hakan ne yayin zantawa da manema labarai a Kano.

Advertisement

NLC Ta Jinjinawa Gwamna Abba Kan Manufofin Tallafa Wa Ma’aikata, Ta Nemi A Ƙara Taimaka Wa Fansho

Goro ya gode wa Allah Madaukakin Sarki da kuma Sanata Kwankwaso bisa damar da aka sake ba shi domin ci gaba da yi wa al’ummar Fagge da jihar Kano hidima.

Advertisement

“Ina matukar godiya ga Allah da ya sake ba ni wannan dama karkashin jagorancin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Haka kuma ina gode wa magoya baya da abokan tafiya bisa irin amincewar da suka nuna mini,” in ji shi.

Ya tabbatar wa al’ummar Fagge cewa tawagarsa za ta dawo da kyawawan ayyukan da aka santa da su a baya tare da kara inganta su domin amfanin jama’a.

Advertisement

“A bisa ikon Allah, za mu dawo da abubuwan alherin da muka yi fice da su tare da kara bunkasa su domin kare muradun al’umma da kuma akidar Kwankwasiyya wadda aka gina domin talakawa,” ya bayyana.

Dan siyasar ya ce tafiyar Kwankwasiyya tana da asali mai karfi a siyasar Kano tun daga zamanin marigayi Aminu Kano, wanda ya bayyana a matsayin ginshikin siyasar talaka a Najeriya.

Advertisement

“A Kano aka gina wannan akida ta siyasa tun daga zamanin Malam Aminu Kano, kuma a wannan lokaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne ke tafiyar da wannan manufa,” in ji Goro.

Da yake mayar da martani kan rade-radin cewa zai iya juya wa Kwankwaso baya idan ya samu nasarar komawa majalisa, Goro ya ce wannan batu ba shi da tushe balle makama.

Advertisement

“Ba gaskiya ba ne. Mun tsaya tare da Kwankwaso tun lokacin da baya cikin gwamnati. Biyayyarmu ba ta da alaka da mukami ko mulki, illa yarda da shugabanci da akidarsa,” ya jaddada.

Goro ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa cewa jam’iyyar NDC za ta samu gagarumar nasara a zabuka masu zuwa, yana mai cewa magoya bayan Kwankwasiyya sun hada kai domin tabbatar da nasarar tafiyar.

Advertisement

Ya kara da cewa yana fatan ganin Kwankwaso ya kai matakin mataimakin shugaban kasa kafin daga bisani ya nemi shugabancin Najeriya.

A bangaren matasa kuwa, Goro ya ce ya fara tsara hanyoyin samar da ayyukan yi domin rage matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasan yankin.

Advertisement

“Mun fara duba hanyoyin samar da ayyukan yi ga matasa. Wasu daga cikin wadanda muka taimaka musu samun aiki a baya yanzu sun kai manyan mukamai a wuraren aikinsu,” in ji shi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending