Connect with us

News

‎Cin Hanci Ne Gidajen Da Shugaba Tinubu Ya Gina Wa Manyan Alkalai A Abuja ‎ ‎—Dr. Hakeem Baba

Published

on

1743757502888

‎Shugaban Jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP), Dakta Hakeem Baba Ahmed, ya soki gina gidajen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi wa alkalan Kotun Ɗaukaka Ƙara, yana mai cewa matakin na iya haifar da tambayoyi kan ‘yancin bangaren shari’a.

‎A wata hira da ya yi da Trust TV a ranar Laraba, Baba Ahmed ya bayyana cewa duk da muhimmancin inganta rayuwar ma’aikatan gwamnati, bai ga dacewar ware alkalai kaɗai domin samun irin wannan gata ba.

Advertisement

Sharuɗoɗi 14 Da Ke Ƙunshe Cikin Yarjejeniyar Amurka Da Iran

‎Kalaman nasa na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabbin gidaje guda 10 da aka gina domin alkalan Kotun Ɗaukaka Ƙara a yankin Katampe da ke Abuja.

Advertisement

‎“Idan gwamnati na son inganta rayuwar alkalai, abin da ya fi dacewa shi ne ta ƙara musu albashi da sauran haƙƙoƙinsu domin su iya mallakar gidajensu da kansu,” in ji Baba Ahmed.

‎Ya ce gina gidaje na musamman ga alkalai, alhali akwai sauran manyan ma’aikatan gwamnati kamar likitoci da manyan sakatarori da ba su samu irin wannan gata ba, na iya haifar da cece-kuce a tsakanin jama’a.

Advertisement

‎Tsohon mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa da yaɗa labarai ya ƙara da cewa, da a ce shi ne zai ba alkalan shawara, da ya buƙace su su yi taka-tsantsan wajen karɓar irin waɗannan kyaututtuka.

‎Sai dai gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata sanarwa ba kan waɗannan kalamai zuwa lokacin haɗa wannan rahoto..

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending