News
Ana Zargin Fashewar Bam A Kasuwa A Legas
An shiga firgici a yankin kasuwar takalma da ke Mushin a jihar Legas bayan wata na’urar fashewa da ake zargin bam ce ta tashi, lamarin da ya haddasa tashin hankali na ɗan lokaci tare da jikkata mutum guda.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Fatai Tijani, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Litinin, inda ya bai wa mazauna jihar tabbacin cewa yankin da abin ya faru na cikin cikakken tsaro bayan jami’an tsaro sun gudanar da bincike.
Amurka Ta Dakatar Da Takunkumin Man Fetur Kan Iran
Da yake magana da manema labarai a Mushin, Tijani ya ce rundunar ’yan sanda ta samu rahoton fashewar ne cikin gaggawa, lamarin da ya sa aka tura jami’an sashen kula da abubuwan fashewa (EOD) domin killace wurin da kuma tabbatar da tsaron jama’a.
A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa fashewar ta samo asali ne daga wata na’urar fashewa ta IED da aka dasa a ƙarƙashin wata mota, inda ta tashi lokacin da aka kunna motar.
Ya bayyana cewa an sanya na’urar ne a gefen kujerar fasinja ta motar, yayin da fashewar ta yi sanadin jikkatar mutum guda, wanda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.
Kwamishinan ya ƙara da cewa ƙwararrun jami’an EOD sun sake gudanar da bincike a yankin bayan aukuwar lamarin, amma ba su gano wata ƙarin na’urar fashewa ba.
Ya ce an tattara ragowar kayan da suka haddasa fashewar domin ci gaba da gudanar da bincike, tare da gano waɗanda ke da hannu a lamarin.
Tijani ya yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da yin watsi da rahotannin da ke nuna cewa tsaro ya taɓarɓare a Legas, yana mai cewa hukumomin tsaro na ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kuma sake jaddada aniyar rundunar ’yan sanda ta tabbatar da zaman lafiya a faɗin jihar, tare da gargaɗin masu aikata laifuka da su guji Legas ko kuma su fuskanci hukunci bisa doka.
