Connect with us

News

Gwamnatin Kano Ta Rufe Kwalejojin Koyon Harkokin Lafiya Biyu

Published

on

Mun daina rusau sai dai mu kai mutum kurkurku kai tsaye Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano ta rufe wasu kwalejojin koyon harkokin lafiya guda biyu da ke karamar hukumar Nasarawa bisa zargin karya doka, ƙa’idojin aiki da kuma rashin cika sharuddan gudanar da irin waɗannan makarantu.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya fitar.

Advertisement

Mazauna Dorayi Sun Ƙalubalanci Shirin Buɗe Film House A Cikin Unguwa, Sun Miƙa Ƙorafi Ga Hukumomi 

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne bayan bincike da tantancewa da ya nuna cewa makarantun suna gudanar da ayyukansu ba tare da izini ba.

Advertisement

Makarantun sun haɗa da IBN SINA College of Health Science and Technology da ke Dakata Kawaji kusa da Masallacin Juma’a, da kuma Life Line College of Health Science and Technology da ke Dakata Industrial Area, Bela Road, Tsamiyar Gare, kan titin Mai Sikeli.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending