Connect with us

News

Iran Ta Ayyana Hutun Kwanaki Uku A Tehran Domin Jana’izar Ali Khamenei

Published

on

IMG 20260623 203138 875

Iran ta ayyana hutun kwanaki uku a babban birnin kasar, Tehran, don gudanar da jana’izar marigayi Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, Ayatollah Ali Khamenei, kamar yadda gidan talabijin na gwamnati ya ruwaito.

“Za a gudanar da taron bankwana da sallar jana’izar gawar jagoran da ya yi shahada a ranar Asabar da Lahadi, 4 da 5 ga Yuli, a Babban Masallacin Mosalla na Tehran, sannan za a yi jana’izar a ranar Litinin, 6 ga Yuli. Saboda haka, za a ba lardin Tehran hutun kwanaki uku,” in ji kwamandan rundunar IRGC mai kula da shirye-shiryen jana’izar, Hassan Hassanzadeh.

Advertisement

Ba Wanda Ya Isa Yace Mana Ga Yadda Zamu Sarrafa Kudadenmu Da Amurka Ta Dagewa Takunkumi – Iran

Mahukuntan Tehran na sa ran kimanin mutane miliyan 20 za su halarci jana’izar.

Advertisement

Har ila yau, birnin Qom da ke arewacin kasar zai karbi bakuncin taron girmamawa ga Khamenei a ranar 7 ga Yuli.

Za a binne Ali Khamenei a ranar 9 ga Yuli a birnin Mashhad da ke arewa maso gabashin Iran, wanda kuma shi ne garin da aka haife shi.

Advertisement

Wadannan birane biyu ma za su yi hutu domin gudanar da bukukuwan.

Makwabciyar kasar Iraƙi ma ta tsara nata bukukuwan na tunawa da Khamenei a ranar 8 ga Yuli.

Advertisement

Tun da farko an shirya gudanar da jana’izar ne a watan Maris, amma aka dage ta sakamakon yakin Gabas ta Tsakiya da ya biyo bayan hare-haren Amurka da Isra’ila na watan Fabrairu, wadanda suka kashe Khamenei.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending