Connect with us

News

An Daure Auren ‘Yar Farfesa Garba Sambo A Kano, An Yi Wa Ma’auratan Fatan Alheri

Published

on

IMG 20260626 WA0015
Advertisements
ads

An gudanar da daurin auren Hafsat Garba Sambo, ‘yar Farfesa Garba Sambo, da angonta cikin walwala a ranar Juma’a, 26 ga Yunin 2026, a Masallacin Juma’a da ke Farawa Layout, Audu Bako Street, bayan Ibrahim Kunya Estate a jihar Kano.

An gudanar da daurin auren ne bayan kammala sallar Juma’a, inda malamai suka jagoranci bikin bisa koyarwar addinin Musulunci, tare da halartar ‘yan uwa, abokai da sauran masu taya iyalan murna.

Ranar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya: Ƙungiyoyi Sun Buƙaci Haɗin Kan Al’umma Don Ceto Matasa a Kano

Bayan kammala daurin auren, mahalarta taron sun yi addu’o’in neman albarka ga sabon gidan auren, inda suka roƙi Allah Madaukakin Sarki Ya sanya zaman auren ya kasance mai cike da soyayya, fahimtar juna, hakuri da kwanciyar hankali.

Sun kuma yi fatan Allah Ya ba ma’auratan zuri’a ta gari, Ya yalwata musu arziki, Ya kare su daga duk wani abu da ka iya kawo cikas ga rayuwar aurensu.

Daurin auren ya gudana cikin natsuwa da farin ciki, yayin da baki da dama suka bayyana fatan ganin ma’auratan sun gina gida nagari da zai kasance abin koyi ga al’umma.

Advertisement

Allah Ya albarkaci wannan aure, Ya tabbatar da zaman lafiya, soyayya da ɗorewar alheri tsakanin ango da amarya. Amin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending