News
Iyalan Mafarauta 16 Da Aka Yi Ajalin Su A Edo Sun Koka Kan Jinkirin Biyan Su Diyya

Iyalan mafarauta 16 ‘yan asalin Jihar Kano da aka kashe a garin Uromi na Jihar Edo a watan Maris na shekarar 2025 sun bayyana damuwarsu kan yadda har yanzu ba a cika alkawuran biyan diyya da tabbatar da adalci da gwamnatocin Kano da Edo suka yi musu ba.
An kashe mafarautan ne yayin da suke kan hanyarsu ta dawowa Kano daga Jihar Rivers domin gudanar da bukukuwan Sallah, bayan wasu fusatattun matasa sun yi musu zargin satar mutane.
CBN Ya Soke Lasisin Bankunan Microfinance 46
Sai dai daga bisani bincike ya tabbatar da cewa zargin da aka yi musu ba shi da tushe, lamarin da ya jawo kira daga bangarori daban-daban na ganin an hukunta masu hannu a kisan.
Wasu daga cikin iyalan mamatan, ciki har da Khadija Abdullahi Hamisu da Aisha Abdullahi, sun ce har yanzu suna rayuwa cikin matsin tattalin arziki bayan rasa masu ciyar da iyalansu.
Sun ce duk da alkawuran da gwamnatocin Kano da Edo suka dauka na biyan diyya da tabbatar da adalci, babu wani gagarumin ci gaba da suka gani ya zuwa yanzu.
A nata bangaren, Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa tana ci gaba da tattaunawa da Gwamnatin Jihar Edo domin ganin an cika alkawarin biyan diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa.
Haka kuma gwamnatin ta ce ta raba tallafin kudi da kayan abinci da darajarsu ta kai kimanin naira miliyan 7.4, inda kowanne daga cikin iyalan mamatan ya samu naira dubu 300, yayin da wadanda suka tsira daga harin suka karbi naira dubu 200 tare da kayan abinci.
Sai dai iyalan mamatan sun ce duk da godiyarsu kan tallafin, hakan bai kai matsayin diyya da adalcin da aka yi musu alkawari ba.
A halin yanzu, kungiyoyin fararen hula da masu rajin kare hakkin dan Adam na ci gaba da kira ga hukumomi da su gaggauta gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a kisan domin tabbatar da adalci.
Kazalika, jaridar SOLACEBASE ta ruwaito cewa ta yi kokarin jin ta bakin Gwamnatin Jihar Edo kan lamarin, amma ba ta samu damar tattaunawa da jami’anta ba kafin kammala wannan rahoto.
