Connect with us

News

Har yanzu akwai matsalolin da suka haddasa yakin basasar Najeriya a shekarar 1970 – Obasanjo

Published

on

obasanjo 2

Tsohon Shugaban Ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa har yanzu akwai wasu daga cikin matsalolin da suka haddasa yaƙin basasar Najeriya na tsakanin shekarun 1967 zuwa 1970, yana mai gargaɗin cewa wajibi ne gwamnati da ‘yan ƙasa su ɗauki matakan da za su hana sake afkuwar irin wannan rikici.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi wasu littattafai, rahotannin bincike da shaidun gani da ido da suka shafi Kisan Gillar Asaba (Asaba Massacre) a ɗakin karatunsa na Olusegun Obasanjo Presidential Library da ke Abeokuta.

Har yanzu akwai matsalolin da suka haddasa yakin basasar Najeriya a shekarar 1970 – Obasanjo

Tsohon shugaban ƙasar ya ce duk da cewa yaƙin basasar ya ƙare sama da shekaru 50 da suka gabata, har yanzu akwai wasu dalilan da suka haifar da rikicin da ke ci gaba da bayyana a fannoni daban-daban, lamarin da ke buƙatar kulawa ta musamman domin tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya.

Ya jaddada cewa sake afkuwar yaƙin basasa abu ne da babu wani ɗan Najeriya da zai yi fatan gani, yana mai cewa ƙasar ta riga ta fuskanci mummunan bala’in yaƙin basasa sau ɗaya, don haka bai kamata a bari tarihi ya sake maimaita kansa ba.

Obasanjo ya yi kira ga shugabanni da al’ummar Najeriya da su fifita adalci, haɗin kai da tattaunawa wajen warware sabanin da ke tsakanin al’umma, domin kare zaman lafiya da tabbatar da haɗin kan ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending